Jirgin Saman Sojojin Najeriya Ya Yi Hatsari A Jihar Neja

Jirgin Saman Sojojin Najeriya Ya Yi Hatsari A Jihar Neja

  • Wani jirgin sojin sama mai saukar angulu mai lamba MI-171 ya yi hatsari a lokacin da yake aikin jigilar mutane zuwa jihar Kaduna daga Neja
  • A wata sanarwa da kakakin rundunar sojin sama Edward Gabkwet ya fitar, an bayyana cewa jirgin ya yi hatsari ne jim kaɗan bayan tashinsa
  • Ana ci gaba da aikin ceto mutanen da ke cikin jirgin duk da har yanzu ba a tantance adadin wadanda suka mutu ba

Minna, jihar Neja - Wani jirgin sojojin saman Najeriya mai saukar angulu, mai lamba MI-171 ya yi haɗari a jihar Neja.

Lamarin dai ya faru ne da misalin ƙarfe 1 na ranar Litinin kusa da ƙauyen Chukuba da ke jihar, kamar yadda mai magana da yawun rundunar sojin saman Edward Gabkwet ya bayyana.

Jirgin sojin saman Najeriya ya yi hatsari a Neja
Jirgin sojin saman Najeriya mai saukar angulu ya yi hatsari a Neja. Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Jami'an Hukumar Kwastam Sun Kama Harsasai 1,245 Da Aka Boye Cikin Buhunan Shinkafa 'Yar Waje

Ina jirgin sojin saman da ya yi hatsari zai je?

An bayyana cewa jirgin ya taso ne daga wata makarantar Firamare da ke Zungeru ta jihar Neja, wanda ya taso ne da zummar zuwa Kaduna.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai jim kaɗan bayan tasowarsa ne ya gamu da haɗari a kusa da wani ƙauye da ake kira Chukuba da ke ƙaramar hukumar Shiroro da ke jihar ta Neja.

Rahoton Channels TV ya bayyana cewa har yanzu ba a tantance adadin mutanen da suke kan jirgin da asalin inda suka fito ba.

Jirgin sojin sama ya yi hatsari a Makurdi

A watan da ya gabata ne aka samu hatsari wani jirgin atisaye mallakin rundunar sojin saman Najeriya a Makurdi da ke jihar Benue.

Sai dai mutane biyun da ke cikin jirgin sun yi nasarar tsira da rayuwarsu kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Wani Dan Fashi Da Makami Da Aka Kama Ya Ambaci Sunan Sifetan 'Yan Sandan Da Ke Basu Bindigu

An bayyana cewa yanzu haka suna karɓar magani da kuma samun kulawar jami'an lafiya a wani asibiti da ke Makurdi.

Dakarun sojin sama sun kashe Ado Aliero da Dankarami

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan luguden wutar da jami'an rundunar sojin saman Najeriya suka yi da ya yi sanadiyyar halaka ƙasurguman 'yan ta'adda a zamfara.

Luguden wutar dakarun sojin saman ta yi sanadin kashe riƙaƙƙun 'yan ta'adda guda biyu, Ado Aliero, da kuma Dankarami, waɗanda suka addabi wasu yankuna na jihar ta Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng