APC Ta Bayyana Cewa Ba Za Ta Hana Kwankwaso Shiga Jam'iyyar Ba, Ta Nemi Hadin Kai

APC Ta Bayyana Cewa Ba Za Ta Hana Kwankwaso Shiga Jam'iyyar Ba, Ta Nemi Hadin Kai

  • Jam'iyyar APC ta bayyana cewa ba za ta hana Sanata Rabiu Kwankwaso shiga cikinta ba
  • Jigo a jam'iyyar, Uche Nwosu shi ya bayyana haka yayin kai ziyarar goyon baya ga shugaban jam'iyyar, Abdullahi Ganduje
  • Ya ce ba abin mamaki ba ne a ga Ganduje da Kwankwaso na sulhu don gyara siyasar kasar da kuma jihar Kano

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Wani jigo a jam'iyyar APC mai mulki, Uche Nwosu ya ce shugaban jam'iyyar, Abdullahi ba zai hana Rabiu Kwankwaso shiga APC ba.

Ya ce haka kuma tsohon gwamnan jihar Kano ba zai hana duk wani mai sha'awar shiga jam'iyyar ba inda ya ce babu wanda ya mallaki jam'iyyar.

APC ta ce ba za ta hana Kwankwaso shiga jam'iyyar ba
Jam'iyyar APC Ta Bayyana Matsayarta Kan Shigowar Kwankwaso. Hoto: Abdullahi Ganduje, Rabiu Kwankwaso.
Asali: Facebook

Me jam'iyyar APC ta ce kan Kwankwaso?

Nwosu ya bayyana haka ne yayin kai ziyarar goyon baya ga Dakta Ganduje ga 'yan jaridu a Abuja, Leadership ta tattaro.

Kara karanta wannan

Shugaba a APC Ya Rubutawa Tinubu Wasika, Ya ce ‘Gwamnatinka Ta Ba Mu Kunya’

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa Ganduje zai ji dadi da farin ciki idan mutane na shiga jam'iyyar saboda hakan ci gaba zai karawa APC, cewar Daily Trust.

A cewarsa:

"Tabbas suna da matsala a tsakaninsu amma babu wanda ya mallaki jam'iyya shi kadai.
"Shigowar Kwankwaso APC zai taimaki Ganduje a Kano, ba abun mamaki ba ne ka gansu tare suna sulhu.
"Za ta iya faruwa ga kansu suna neman gyara tsakaninsu a siyasance don kara tabbatar da karfin dimukradiyya a kasar."

APC ta yi tsokaci kan mulkin dimokradiyya

Ya kara da cewa:

"Lalataccen tsarin dimokradiyya yafi mafi kyawun mulkin soja a ko ina a duniya."

Ya ba da misalin abin da ke faruwa a Jamhuriyar Nijar da cewa abin takaici ne, inda ya ce duk lalacewa gwara siyasa da ke kusa da mutane.

Ya roki 'yan Najeriya da su yi hakuri da shugaban kasa, Bola Tinubu na shekara daya kafin su yanke masa hukunci, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Shugabannin APC Da Dama Sun Yi Murabus Daga Kujerunsu a Wata Jihar Arewa

APC Ta Nada Ganduje A Matsayin Shugabanta

A wani labarin, jam'iyyar APC mai mulki ta zabi Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar na kasa baki daya.

Jam'iyyar ta tabbatar da haka ne yayin ganawa ta masu ruwa da tsaki a Abuja wanda ya samu halartar Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima da sauran manyan 'yan jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.