Jam'iyyar PDP Ta Bankado Shirin Jam'iyyar APC Na Fara Yaki Da Nijar

Jam'iyyar PDP Ta Bankado Shirin Jam'iyyar APC Na Fara Yaki Da Nijar

  • Jam'iyyar PDP ta bankaɗo shirin jam'iyyar APC na son afkawa Jamhuriyar Nijar da yaƙi kan juyin mulkin da aka yi a ƙasar
  • PDP ta zargi jam'iyyar APC da Shugaba Tinubu da son fara yaƙi da Nijar domin tsokalo ƙasar ta mayar da martani
  • A cewar zargin na jam'iyyar PDP hakan zai sanya a kafa dokar ta ɓaci ta yadda za a dakatar da kotun zaɓe sanar da hukuncin shari'ar zaɓen shugaban ƙasa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana cewa Shugaba Tinubu da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun amince su sanya ƙasar nan cikin yaƙi kan rikicin siyasar da ke faruwa a Jamhuriyar Nijar.

A cikin wata sanarwa da kakakin jam'iyyar PDP, Debo Ologunagba, ya rattaɓawa hannu, an zargi gwamnatin APC da sanya dakarun Najeriya cikin faɗan da ba a buƙatar shi da Jamhuriyar Nijar.

Kara karanta wannan

Amurka Ta Yi Gargaɗi Mai Zafi Ga Sojojin Nijar Kan Taba Lafiyar Bazoum Da Ta Iyalansa

PDP ta zargi APC da son yin yaki da Nijar
PDP ta bankado shirin APC kan Nijar Hoto: @OfficialPDPNig @DOlusegun
Source: Twitter

A cikin sanarwar wacce aka sanya a shafin jam'iyyar na Twitter a ranar Lahadi, 13 ga watan Agusta, Ologunagba ya bayyana cewa jam'iyyar ta yi Allah wadai da abinda ta kira son shiga yaƙi na Tinubu da APC.

APC da Tinubu na son kawo hargitsi

A cewar jam'iyyar PDP, haƙiƙancewar Shugaba Tinubu na tura sojojin Najeriya zuwa Nijar duk da rashin amincewar majalisar tarayya da ƴan Najeriya, shaida ce mai nuna cewa shugaban ƙasar yana son kawo hargitsi ne a ƙasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai, jam'iyyar PDP ta nuna rashin jindaɗinta kan juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar amma ta haƙiƙance cewa halin da ake ciki a ƙasar bai kai a tura dakarun Najeriya ba domin kwantar da tarzoma a ƙasar.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

Kara karanta wannan

Juyin Mulkin Nijar: Kungiyar CAN Ta Faɗawa Tinubu Ainihin Matakin Da Ya Kamata Ya Ɗauka

"Jam'iyyar APC ta ƙosa ne kawai ta tura sojojin Najeriya zuwa Nijar domin tsokalo ƙasar faɗa ta yadda za su mayar da martani. Yin hakan zai sanya a kafa dokar ta ɓaci a Najeriya da niyyar daƙile shari'ar da ake gudanarwa kan zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023."

Tchiani Ya Amince Zai Tattauna Da ECOWAS

A baya rahoto ya zo cewa shugaban sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya amince zai tattauna da ƙungiyar ECOWAS.

Amincewar da Tchiani ya yi domin hawa kan teburin sulhu da ECOWAS ta zo ne bayan ya gana da malaman addinin musulunci daga Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng