‘Yan Kasuwa sun yanke litar man fetur ya tashi daga N620 zuwa N720 a Najeriya

‘Yan Kasuwa sun yanke litar man fetur ya tashi daga N620 zuwa N720 a Najeriya

  • A lissafin da ake yi, kudin sayen litar man fetur zai iya tashi nan da wasu ‘yan kwanaki a kasar nan
  • Dillalai su na hasashe tsakanin N680 da N720 a dalilin yadda kasuwa ta canza a halin da ake ciki a yau
  • Gagarumin tashin Dalar Amurka zuwa kusan N950 a kasuwar canji zai shafi farashin gidajen mai

Abuja - A ranar Lahadi, dillalan mai su ka nuna farashin man fetur zai iya komawa tsakanin N680 zuwa N720 a kan kowane lita a Najeriya.

Punch ta ce karin ya zo ne a sakamakon tashin da Dalar Amurka tayi a kasuwar canji, ‘yan kasuwa su na sayen duk $1 kan N910 zuwa N950.

Dillalan sun kuma nuna dole wasu su ka hakura da shigo da fetur saboda karancin kudin kasar waje da ake bukata domin ciniki a ketare.

Kara karanta wannan

Dalla-dalla: Kamfanoni sama da 10 da baku san mallakin CBN bane a Najeriya

Fetur
Hoton tankokin man fetur a Faransa Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana bukatar $30m daga CBN

Abubuwa sun tsaya cak a kafar CBN da ake samun Dala a kan N740 a Najeriya. Dillalan mai su na bukatar $25m zuwa $30m daga bankin.

Rahoton ya ce ‘yan kasuwan da su ka shigo da man kwanan nan su na shan wahala wajen maida ribarsu duk saboda karyewa da Naira ta yi.

Manyan ‘yan kasuwa sun nuna ya zama dole gwamnatin tarayya ta tsoma baki a lamarin yayin da Bola Tinubu ke kokarin janye hannunsa.

Shigo da fetur ya zama aiki

Mai magana da yawun kungiyar IPMAN na kasa, Cif Chinedu Ukadike ya ce da zarar Naira ta karye a kan Dala, dole hakan zai shafi farashinsu.

Clement Isong wanda babban ‘dan kasuwan ne da ke harkar mai, ya ce duk da an kara lasisin shigo da fetur, dillalai sun tsaida sayo shi daga waje.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Malaman Izala sun dira Nijar don neman hanyar sulhu a batun juyin mulki

Vanguard ta ce alamu sun nuna za a gamu da wani sabon karin farashi a gidajen mai domin wadanda su ka shigo da mai sun gamu da tsada.

Lissafin da aka yi ya nuna kudin dako da shigo da fetur zuwa Najeriya ya karu da 37.4%. A haka ana cewa mai ya na da araha a kasar nan.

Daga N460 da aka shigo da lita a watan Yunin 2023, a Yuli farashin ya koma N632.17. a haka ba a maganar kudin kai fetur zuwa gidajen man kasar.

Litar N190 ta harba zuwa N620

Kwanakin baya an rahoto kungiyar IPMAN ta ‘yan kasuwan mai su ka yi watsi da jita-jitar da ke yawo a kan batun karin kudin litar man fetur.

A karshe dai an yi karin, yanzu haka ana saida fetur a kan kusan N620. Wannan ya na cikin sauye-sauyen da ake gani daga gwamnati mai-ci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng