“Akwai Bala'in Da Ya Kusa Faɗawa Najeriya Da Ba Mu Karbe Mulki Ba”, Tchiani Ya Yi Bayani
- Shugaban mulkin sojin jamhuriyar Nijar, ya bayyana yadda juyin mulkin ya amfani Najeriya
- Janar Abdourahmane Tchiani ya bayyana cewa juyin mulkin da suka yi ya ceci Nijar da Najeriya daga faɗawa wani bala'i
- Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya tarbi tawagar malaman addinin Musulunci daga Najeriya
Niamey, Nijar - Shugaban mulkin sojin jamhuriyar Nijar, Abdourahmane Tchiani, ya bayyana cewa, juyin mulkin da suka yi ya ceci Najeriya daga faɗawa bala'i.
Ya bayyana hakan ne ranar Asabar, a yayin da yake zantawa da manyan malaman addinin Musulunci, da Sheikh Bala Lau ya jagoranta daga Najeriya zuwa Nijar.
Malaman sun zarce jamhuriyar Nijar ne bayan ganawarsu da Shugaba Bola Tinubu a ranar Juma'a kamar yadda Daily Trust ta wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda juyin mulkin ya ceci Najeriya
Sheikh Bala Lau ya bayyana cewa, Tchiani ya shaida musu cewa an gudanar da juyin mulkin cikin nasara, wanda hakan ya kare ba iya Nijar ba, har ma Najeriya daga wani bala'i da ya tunkarosu.
Sai dai shugaban sojojin juyin mulkin bai bayyana takamaiman bala'in da yake nufi ya tunkaro ƙasashen ba.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da cewa ba za ta yi wa gwamnatin Tinubu juyin mulki ba kamar yadda wasu suka buƙata.
Rundunar tsaro za ta ci gaba da kiyaye dimokuraɗiyyar Najeriya
Daraktan yaɗa labarai na hukumar tsaron Najeriya, Birgediya Janar Tukur Gusau ya bayyana cewa, akwai wasu mutane da ke ƙoƙarin ingiza sosojin Najeriya wajen ganin sun kifar da gwamnatin Tinubu.
Ya bayyana cewa zugar da ake yi wa rundunar ba za ta yi tasiri ba, inda ya ce jami'an sojin Najeriya za su ci gaba da kare dimokuraɗiyya maimakon ƙoƙarin kawar da ita.
Ya ƙara da cewa wasu marasa kishin ƙasa ne ke ƙoƙarin ganin an gudanar da juyin mulki a Najeriya kamar yadda The Street Journal ta wallafa.
An yi zanga-zanga kan shirin ECOWAS a Kano
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan zanga-zangar da aka gudanar a birnin Kano domin nuna adawa da yaƙin da yake neman ɓarkewa tsakanin Najeriya da Nijar.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyar ECOWAS take ƙara ƙaimi wajen yin amfani da ƙarfin soji domin dawo da dimokuraɗiyyar jamhuriyar Nijar.
Asali: Legit.ng