An Samu Rabuwar Kai a Majalisar ECOWAS Kan Batun Daukar Matakin Soji Kan Shugabannin Sojin Nijar
- A halin da ake ciki, majalisar ECOWAS ta samu tsaiko kan matsayar da ya kamata a dauka kan sojin Nijar
- Wasu sun bayyana rashin goyon bayansu ga matakin da ake son dauka na tura su yaki masu juyin mulkin Nijar
- A yanzu, kungiyar Izala ta tafi Nijar don tattaunawa da shugabannin mulkin sojin kasar don neman sulhu
Majalisar Tarayyar Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS) ta samu rarrabuwar kai kan matakan da ya kamata a dauka domin warware juyin mulkin Nijar.
Yayin da wasu 'yan majalisar ta ECOWAS ke goyon bayan a dauki matakin soji a kan gwamnatin sojin Nijar, wasu kuma sun nuna adawa da hakan, Vanguard ta tattaro.
'Yan majalisar daga kasashe 22 ne suka halarci taron na musamman na yau Asabar 12 ga watan Agusta domin tattauna lamarin da ke kara tsami a Jamhuriyar Nijar.
Sabanin da aka samu a tsakanin 'yan majalisar ECOWAS
Yayin da wasu daga cikin ‘yan majalisar suka ba da shawarin tattaunawa da bin lallabin diflomasiyya, wasu kuma sun yi kira da a dauki matakan da za su dakile yunkurin kifar gwamnatoci daga sojoji a nahiyar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ali Djibo, dan majalisar ECOWAS daga Jamhuriyar Nijar ya ce tuni aka rufe akalla makarantu 9,000 sakamakon rikicin da kasar ke fuskanta a yanzu.
Ya kuma bayyana yadda kasar ke fuskantar matsalar shige-da-ficen kayayyaki sakamakon juyin mulkin da kuma kakaba takunkumi kan kasar.
A dai bi a hankali
Awaji-Inombek Dagomie Abiante (daga jihar Rivers a Najeriya), ya ce dole ne ECOWAS ta mai da hankali sosai tare da gano musabbabin juyin mulki a kasashenta.
Mambobin Majalisar ta ECOWAS da ke gabatar da jawabi sun ce lallabin diflomasiyya ya taimaka wajen karuwar mamayar da sojoji ke yi a yankin Yammacin Afirka, TVP ta tattaro.
Da yake bayar da gudunmuwa, Adebayo Balogun, ya bayyana cewa shugabannin ECOWAS suna ba da shawarar daukar matakin soji ne don kawar da mulkin soja ba wai yunkuri ne na cikakken yaki da kasar ba.
Nijar ta rattaba yarjejeniya da ECOWAS
Ya tunatar cewa Nijar ta kasance kasar da ta rattaba hannu kan yarjejeniyar kungiyar ECOWAS da aka yi wa hana tsoma bakin soja a lamarin mulki.
A bangare guda, Bashir Dawodu ya bayyana ra'ayinsa cewa ya kamata kungiyar ta bayyana kanta kan yiwuwar daukar matakin soja tare da matsa lamba kan tabbatar da dawo da mulkin dimokradiyya.
A bangare guda, fitattun malaman addinin Musulunci karkashin jagorancin shugaban kungiyar Jama’a tul Izalatil Bid’ah wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta kasa Sheikh Bala Lau, sun dira jamhuriyar Nijar a wani mataki na neman hanyar da za ta sa a sasanta lamarin da ya faru na juyin mulki.
A hotunan da Legit.ng Hausa ta gani a shafin Twitter na kafar Zagazola Makama, an ga lokacin da malaman suka sauka a Nijar.
An gano malaman a filin jirgin sama, inda suka samu tarba daga jami’an sojin jamhuriyar ta Nijar da ke makwabataka da Najeriya.
Asali: Legit.ng