Hambararren Shugaban Nijar Bazoum Ya Samu Damar Ganin Likitansa a Karon Farko Bayan Kwace Mulkinsa

Hambararren Shugaban Nijar Bazoum Ya Samu Damar Ganin Likitansa a Karon Farko Bayan Kwace Mulkinsa

  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, an gano yanayin da tsohon shugaban Nijar, Mohamed Bazoum ke ciki a yanzu
  • Likitan Bazoum ya samu ganinsa, inda ya tabbatar da cewa yana cikin koshin lafiya a halin da ake ciki
  • An hambarar da gwamnatin Bazoum a watan Yuli biyu bayan wani juyin mulkin da sojojin kasar suka yi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Yamai, Nijar - Hambararren shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum, wanda dakarun juyin mulkin karkashin jagorancin Janar Abdourahamane Tchiani ke tsare da shi tun watan Yuli ya samu damar ganin likitansa a ranar Asabar.

An gano cewa, likitan ya kuma kawo wa Bazoum tare da matarsa da dansa abinci a inda sojojin ke ci gaba da tsare su.

Wani mamba a tawagarsa ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP cewa hambararren shugaban tabbas ya samu ganin likitan nasa.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Malaman Izala sun dira Nijar don neman hanyar sulhu a batun juyin mulki

Bazoum ya samu ganin likita
Bazoum ya samu ganin likitansa a karon farko | Hoto: Channels Tv
Asali: Twitter

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Yana cikin koshin lafiya, duba da halin da ake ciki."

Halin da ake ciki a baya

An dai shiga damuwa kan yanayin lafiyar Bazoum da matarsa da dansa mai shekaru 20 tun bayan da sojoji suka kwace mulkin kasar tare da kama su a ranar 26 ga watan Yuli, DW ta tattaro.

Kungiyar Tarayyar Turai (EU) da Tarayyar Afirka (AU) sun bi sahun wasu kungiyoyin duniya wajen yin Allah wadai da hambarar da Bazoum da kuma tsare shi da sojojin kasar suka yi.

Babban jami'in kare hakkin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk ya ce tsare Bazoum da aka yi ka iya zama cikin wulakanci da cin mutunci.

An take hakkin Bazoum

Hakazalika, ya bayyana cewa, ci gaba da tsare Bazoum din tabbas ya saba wa dokar kare hakkin bil'adama.

Kara karanta wannan

Turo soji su yaki Nijar: 'Yan wata jihar Arewa a Najeriya sun fara zanga-zangar adawa da ECOWAS

Babban jami'in diflomasiyyar Amurka Antony Blinken ya ce ya ji takaici ainun da kin sakin dangin Bazoum da sojoji suka yi.

Sojin Najeriya sun fi na Nijar, inji jigon APC

A wani tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya yi wani kakkausan gargadi ga shugabannin mulkin soja a Nijar, Mali da Burkina Faso kan abin da ya bayyana a matsayin barazana ga Najeriya.

Jigon na jam’iyyar APC mai mulki ya bukaci shugabannin da suka yi juyin mulki da kada su tunzura Najeriya a yanayi irin wannan.

Bayan juyin mulkin da aka yi a jamhuriyar Nijar a baya-bayan nan da ya hambarar da shugaban kasar Mohamed Bazoum, ECOWAS, ta ba gwamnatin mulkin soji a Nijar wa'adin kwanaki bakwai da ta dawo da hambararren shugaban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.