Obasanjo Ya Bayyana Malamin Addinin Kiristocin Najeriya Daya Tak Da Zai Shiga Aljanna

Obasanjo Ya Bayyana Malamin Addinin Kiristocin Najeriya Daya Tak Da Zai Shiga Aljanna

  • Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban kasar Najeriya, ya ce marigayi Prelate Emeritus na Cocin Methodist da ke Najeriya, Dakta Sunday Mbang ne kadai shugaban kiristocin Najeriya da zai shiga aljanna
  • A cewar Obasanjo, Dr Sunday Mbang mutum ne tsayayye kuma ba mai amfani da shauki wurin daukan matakai ba yayin da ya ke raye
  • Tsohon shugaban kasar kuma ya bayyana cewa yana neman shawarar marigayin a kan muhimman batutuwa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Uyo, Akwa Ibom - Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya yi wani magana mai nauyi inda ya bayyana wanda zai shiga aljanna a cikin shugabannin kiristocin Najeriya.

Tsohon shugaban kasar ya ce malamin addini na Najeriya guda daya tak da ya ke da tabbacin zai shiga aljanna shine Dakta Sunday Mbang, CON, marigayi Prelate Emeritus na Cocin Methodist da ke Najeriya, PM News ta rahoto.

Kara karanta wannan

An Sha Shagalin Bikin Dan Majalisar Kaduna, Bello El-Rufai Da Tsaleliyar Amaryarsa, Hotunan Sun Dauki Hankali

Obasanjo ya bayyana malamin addinin kiristan Najeriya daya da zai shiga aljanna
Obasanjo Ya Fadi Shugaban Kiristocin Najeriya Daya Tak Da Zai Shiga Aljanna. Hoto: Olusegun Obasanjo
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kasancewarsa babban bako na muamman a wurin bikin jana'izar marigayin babban malamin addinin a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom, a ranar Juma'a 11 ga watan Agusta.

A cewar tsohon shugaban kasar, marigayin tsayayye ne kuma ba ya amfani da shauki wurin daukan mataki.

Ya bayyana cewa tsohon malamin addinin na daya cikin wadanda ya tuntuba don shawara jim kadan bayan an sako shi daga gidan yari kuma aka bukaci ya zo ya yi takarar shugaban kasa.

Obasanjo ya yi magana kan alakarsa da marigayin shugaban kungiyar ta kiristoci CAN

Obasanjo ya kara da cewa a lokacin da ya ke tuntubar Mbang, ya amfana sosai da shawarwari, ya ce yana neman shawara a wurinsa sosai saboda baya fargabar fada masa gaskiya.

Ya bayyana cewa a wasu lokuta a zamanin tsohon Gwamna Emmanuel Udom, zai ziyarci jihar da sunan ya zo ganin gwamna amma yana son yana son neman shawara ne daga marigayin malamin addinin kan muhimman batutuwa.

Kara karanta wannan

Nijar: ‘Yaki Ba Mafita Bane’, Malamin Addini Ya Bayyana Abun da Zai Faru Idan ECOWAS Da Tinubu Suka Ki Neman Sulhu

Mbang shine mutum bakin fata na farko da ya jagoranci World Methodist Council kuma tsohon shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN. Ya rasu yana da shekaru 86 a garin Uyo ranar Talata 16 ga watan Mayu.

Obasanjo Ya Ce Najeriya Ta Kunyata Kanta, Afrika Da Duniya Baki Daya

A wani rahoton, tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo, ya ce Najeriya ta kunyata kanta da kuma Afrika baki daya.

Ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi wajen kaddamar da wani littafi da tsohon ministan masana'antu da zuba hannun jari, Olusegun Aganga ya rubuta kamar yadda The Punch ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164