Najeriya Ta Fado Mataki Na 3 Wurin Samar Da Mai A Afirka, OPEC Ta Yi Bayani
- Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Mai, OPEC ta fitar sabon jadawalin mambobinta mafi samar da mai din a Afirka
- OPEC ta ce Najeriya ta rasa matakin farko yayin da gangaro har mataki na uku inda Libya ta karbi matakin farko
- Wanna na nuna kasar za ta yi asarar kudaden shiga masu dimbin yawa ganin yadda farashin mai din ya tashi yanzu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Mai (OPEC) ta fitar da rahoto cewa Najeriya ta rasa mataki na daya a Nahiyar Afirka.
OPEC ta ce Najeriya a watan Yuli ta na fitar da gangan mai miliyan daya da dubu 800 a ko wace rana. Legit.ng ta tattaro.

Asali: Facebook
Mataki na nawa Najeriya ta ke?
Kasar ta ci baya wurin samar da gangan mai din idan aka kwatanta da miliyan daya da dubu dari biyu na watan Junin 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar ta bayyana haka ne cikin rahoton da ta fitar na watan Agusta na shekarar 2023.
Gazawar Najeriya ya ba wa kasar Libya zama wacce tafi samar da mai din a Nahiyar da ganga miliyan daya da dubu 171 a rana cikin watan Yuli.
Angola ta ci gaba da rike mataki na biyu a Afirka da ganga miliyan daya da dubu 149 na watan Yuli.
Sauran kasashen Afirka da ke kan gaba sun hada da Algeriya da Congo da Gabon da ke samar da ganga 955,000 da 282,000 da kuma 62,000 a jere.
Me ya jawo wa Najeriya saukowa kasa?
Tun bayan cire tallafin mai da Shugaba Tinubu ya yi, kasar ta shiga cikin mawuyacin hali da kuma raguwar amfani da mai din a kasar.
Daga cikin dalilan kuma akwai satar danyen man fetur wanda Shugaban ya yi alkawarin kawo karshen hakan nan ba da jimawa ba.
A ranar 7 ga watan Yuli an cafke wasu da litar danyen mai 800,000 na sata a jihar Ondo.
Kasashen Da Suka Fi Siyan Mai Da Tsada
A wani labarin, bayan cire tallafin mai a Najeriya, 'yan kasar sun shiga tashin hankali kan tsadar man fetur.
A wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta tattaro muku kasashen Nahiyar Afirka da suka fi siyan man da tsada musamman a wannan yanayi na tashin Dala.
Asali: Legit.ng