“Abun da Na Yi Da Miliyan 20 Da Aka Tura Asusuna Bisa Kuskure,” Dan Bautar Kasa Ya Magantu

“Abun da Na Yi Da Miliyan 20 Da Aka Tura Asusuna Bisa Kuskure,” Dan Bautar Kasa Ya Magantu

  • Adekunle Isaiah Oluwaseun, wani dan bautar kasa, ya ce ya kadu a lokacin da ya samu alat na naira miliyan 20
  • Dan bautar kasar, wanda ke da N1,521 kacal a asusunsa, ya ce baya tsammanin ganin irin wannan makudan kudin
  • Bayan ya bincika sunan wanda ya aika kudin a yanar gizo, matashin ya bayyana matakin da ya dauka, wanda ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani mai yi wa kasa hidima, Adekunle Isaiah Oluwaseun, ya samu shigar naira miliyan 20 a asusun bakinsa a kawanan nan wanda aka tura masa bisa kuskure kuma ya dauki mataki da mutane da dama suka bayyana a matsayin gaskiya.

Matashin wanda ya kammala karatunsa daga jami'ar Lagas ya ce ya kadu sannan ya firgita da ya ga alat din, yana mai cewa N1,521 ne kacal da shi a asusun bankinsa.

Kara karanta wannan

“Miliyan 4 Aka Biya Ni”: Matashi Da Ya Rikide Ya Koma Mace Ya Yi Tafiyar Rangwada Da Takalma Masu Tsini, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Dan bautar kasa ya mayar da miliyan 20 da aka tura asusunsa bisa kuskure
“Abun da Na Yi Da Miliyan 20 Da Aka Tura Asusuna Bisa Kuskure,” Dan Bautar Kasa Ya Magantu Hoto: Igbere TV
Asali: Facebook

Adekunle Isaiah Oluwaseun ya bayyana matakin da ya dauka

A wata hira da Igbere TV, dan bautar kasar, wanda ke hidimar kasarsa a jihar Ogun, karamar hukumar Illesha ta yamma, ya tuna yadda ya mayar da kudin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Isaiah ya ce ya fara neman sunan wanda ya tura da kudin a yanar gizo, bayan ya sanar da mahaifinsa, sannan daga bisani ya samu kiran WhatsAPP daga bankin FCMB reshen Ilupeju. Kiran bankin ya biyo bayan kira daga wani wakilin asibitin ukkha Hospitality LTD, wanda shine ya tura kudin.

A cewarsa, ya ba su tabbacin cewa zai dawo da kudin.

An ba Adekunle Isiah Oluwaseun tukwicin gaskiyarsa

Isaiah, wanda shine shugaban yan bautar kasa a karamar hukumar Illesha ta yamma, ya bayyana cewa wata matashiya daga asibitin Bukkha Hospitality LTD ta tuntube shi, tana mai nuna godiya ga hadin kan da ya basu sannan ta ba shi hakuri a kan shiga lokacinsa da suka yi.

Kara karanta wannan

A gaba na wani ya soye ya mutu: Dalilin da yasa mawaki ya daina aiki a kamfanin Dangote

Ya ce ta tura masa N20k don nuna godiya a gare shi sannan ta nemi ya tura takardunsa da zaran ya kammala hidimar kasarsa.

Isaiah ya kara da cewar har yanzu bai samu kira daga bankin ba bayan ya mayar da kudin.

gaskiyar Isaiah ya haddasa cece-kuce yayin da wasu mutane suka caccake shi, wasu kuma sun jinjina masa.

Jama'a sun yi martani kan lamarin

Orji Mela Chimex ya ce:

"Daga wajenmu kuma a madadin masu gaskiya da amana da tsatsauran ra'ayi maza masu mutunci.....
"Mun taya ka murna, ka ci gaba da wakiltanmu da kyau..."

Michael O. Esezoobo ya ce:

"Wannan ita ce Najeriya da muke so; ko ba yanzu ba, za ka samu tukwici fiye da tunaninka kan wannan abu. Ina fatan mutane da ke hukuma masu daukar duk kudin da suka gani kamar mahaukacin da ke tsince-tsince a titi za su koyi darasi daga nan."

Chika A Michael ya ce:

Kara karanta wannan

Innalillahi: An Tsinci Gawar Hadimin Fitaccen Sanata Da Raunin Harsashi

"Ko da ka mayar ko da baka mayar ba za su dawo da kudinsa sannan ka ta tafi gidan maza. Ban san lokacin da wasu za su fahimci cewa wannan 2023 bane."

Hadadden likita ya tashi kan yan mata

A wani labari na daban, wani likita mai suna Dr Jae, ya dauki hankalin yan mata da dama a soshiyal midiya saboda tsantsar kyawun da Allah ya yi masa.

Lamarin ya fara ne lokacin da Dr Jae ya saki zafafan hotunansa a bakin aiki kan TikTok da taken "Kowa na da rawan ganin da zai taka wannan shine nawa."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng