Jamhuriyar Nijar: Jerin Kasashe 6 Na Afirka Ta Yamma Da ECOWAS Ta Tura Dakarun Soji

Jamhuriyar Nijar: Jerin Kasashe 6 Na Afirka Ta Yamma Da ECOWAS Ta Tura Dakarun Soji

  • Tun bayan hambarar da Mohamed Bazoum a Nijar, kungiyar ECOWAS ke kokarin shawo kan matsalar
  • A karshe ta yanke shawarar daukar matakin soji a kasar bayan wata ganawa na musamman a Abuja
  • Sojojin Nijar sun yi fatali da barazanar ECOWAS tare da sake kafa wata sabuwar gwamnati a kasar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja – Kungiyar Raya Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta na da tarihin mamayar kasashen yankin na karfin soji tun a baya.

A jiya Alhamis 10 ga watan Agusta ne kungiyar ta yi wata ganawa a Abuja tare da ba da umarni ga dakaru su tsaya da shirinsu na afkawa Jamhuriyar Nijar.

Jerin kasashe 6 da kungiyar ECOWAS ta afkawa a Nahiyar Afirka ta Yamma
Jerin Kasashe 6 Na Nahiyar Afirka Ta Yamma Da Suka Fuskanci Dakarun ECOWAS. Hoto: Opinion Nigeria.
Asali: Facebook

Wasu kasashe ECOWAS ta afkawa a Afirka?

Sojojin juyin mulki sun yi fatali ta barazanar ECOWAS tare da nada sabbin ministoci a kasar bayan kifar da Mohamed Bazoum.

Kara karanta wannan

Duk Yaudara ce: Naja’atu Ta Tona Dalilin Shugaba Tinubu Na Tsokano ‘Yaki’ Da Nijar

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wannan karo shi ne na bakwai da kungiyar ke shirin tura rundunar kasashen kungiyar zuwa Nijar idan hakan ta tabbata, Vanguard ta tattaro.

Kungiyar me dauke da kasashe 15 da Najeriya ke jagoranta ta tura dakaru kasashen yankin tun shekarar 1990.

Kasashe nawa ne ECOWAS ta tura dakaru?

1. Liberia

Farkon fara tura dakaru ya kasance ne a watan Agusta na shekarar 1990 a kasar Liberia, Opinion Nigeria ta tattaro.

Kungiyar ta tura dakarun yayin da ake yakin basasa a kasar inda sojojin suka sake shiga kasar a shekarar 1997, yayin da suka bar kasar gaba daya a 1999.

Bayan shekaru hudu ECOWAS ta sake tura dakaru bayan sake barkewar yakin basasa.

2. Saliyo

ECOWAS ta tura dakaru kasar Saliyo bayan barkewar yakin basasa a watan Mayu na shekarar 1997 inda suka samu nasarar korar sojojin juyin mulki tare da dawo da Shugaba Ahmad Tejan Kabbah kan mulki.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: ECOWAS Ta Umurci Sojojinta Su Ɗaura Ɗamarar Yaƙar Sojojin Nijar, Bayanai Sun Fito

3. Giunea Bissau

Bayan sojoji sun hambarar da Shugaba Joao Bernado Vieira a 1999, ECOWAS ta tura sojoji.

Bayan watanni kadan dakarun sun fice daga kasar saboda sun gagara hana hambarar da shugaban.

Rundunar ta sake dawo wa a 2012 bayan samun wani juyin mulki.

4. Ivory Coast

Akalla dakaru 1,300 ne na ECOWAS aka tura kasar a 2003 bayan barkewar yakin basasa.

Dakarun ECOWAS a shekarar 2004 ta samu karfi a kasar bayan hadewa da dakarun Majalisar Dinkin Duniya.

5. Mali

A watan Janairu na 2013, ECOWAS ta tura dakaru kasar don dakile mamayar Al-Qaeda a Arewacin kasar.

Dakarun ECOWAS 6,300 ne suka hade da na Majalisar Dinkin Duniya a kasar don shawo kan matsalar.

Sojojin UN sun fice a 2023 bayan sojoji masu adawa da kasashen Yamma sun fatattake su.

6. Gambia

A watan Janairu na 2017, dakarun ECOWAS sun dira a kasar don tilasta Yahaya Jameh sauka a mulki bayan rashin nasara a zaben da Adama Barrow ya ci.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Asari Dokubo Ya Sha Alwashin Yin Kasa-Kasa Da Gwamnatin Sojan Nijar

Bayan kwanaki biyu, Jammeh ya amince ya nemi mafaka a Equitorial Guinea inda hakan ya kawo karshen matsalar da ta shafe makwanni shida ana yi.

ECOWAS Ta Yanke Shawarar Yakan Nijar

A wani labarin, Kungiyar ECOWAS ta umarci dakarun ta da su daura damarar yakan Jamhuriyar Nijar.

Shugaban hukumar, Aliu Toure shi ya bayyana haka bayan kammala taron da kungiyar ta yi a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.