Rundunar ’Yan Sanda Ta Cafke Matasa 3 Da Suka Hallaka Jami'insu A Jihar Bauchi

Rundunar ’Yan Sanda Ta Cafke Matasa 3 Da Suka Hallaka Jami'insu A Jihar Bauchi

  • Jami’an ‘yan sanda a jihar Bauchi sun kama wasu mutane da ake zargi da kisan wani dan sanda Bala Nazifi Magaji a bakin aiki
  • Kakakin rundunar a jihar, Ahmed Wakili shi ya bayyana haka yayin gabatar da wadanda aka kaman da kisan a karamar hukumar Darazo
  • Wakili ya ce wadanda ake zargin sun hada da Aminu Mohammed da Abdullahi Abubakar da kuma da Balarabe Abubakar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Bauchi – Rundunar ‘yan sandan Bauchi ta cafke wasu mutane uku da ake zargi da kashe dan sanda a karamar hukumar Darazo da ke jihar.

Kakakin rundunar a jihar, Ahmed Wakili shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa inda ya ce an kashe Bala Nazifi Magaji a kauyen Konkiyel da ke karamar hukumar Darazo a ranar 25 ga watan Juli a bakin aiki.

Kara karanta wannan

Abin Kunya Yayin Da Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Wata Ya Da Kanwarta Saboda Satar Man Goge Baki, Alkali Ya Yi Martani

'Yan sanda sun kama wadanda ake zargin da jami'insu a Bauchi
Yan Sanda Sun Kama Matasa 3 Da Zargin Hallaka Jami'insu A Bauchi. Hoto: Tribune.
Asali: Facebook

Ya ce wadanda ake zargin an kama su ne bayan bincike mai zurfi da rundunar ta yi bayan kisan dan sandan da ke bakin aiki, The Guardian ta tattaro.

Su wa 'yan sandan suka kama?

Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Wadanda ake zargin sun hada da Aminu Mohammed da aka fi sani da Kangado mai shekaru 35 da ke unguwar Sarkin Baka Konkiyel.
"Sauran sun hada da Abdullahi Abubakar da aka fi sani da Duna mai shekaru 23 da Balarabe Abubakar mai shekaru 34 yayin da sauran mutum shida ake ci gaba da nemansu.”

Wakili ya ce dukkan wadanda ake zargin sun tabbatar da aikata laifin kashe dan sandan da adduna da kuma sanduna, cewar Vanguard.

Ya aka yi suka yi ajalin dan sandan?

Ya kara da cewa:

“Daya daga cikinsu Aminu Mohammed yayin tabbatar da aikata laifin ya bayyana yadda suka yi amfani da duhun dare suka sare shi a baya da adduna.

Kara karanta wannan

Abin Da Ya Jawowa El-Rufai, Danladi Da Okotete Samun Tasgaro a Zama Ministoci

“Dayan ya yi amfani da duwatsu da sanduna suka buga masa a kai, dalilin haka ya samu raunuka tare da rasa jini mai tarin yawa.
“An dauki dan sandan zuwa babban asibitin Darazo inda wani likita ya tabbatar da rasuwarshi.”

Har ila yau, rundunar ta bazama neman sauran wadanda ke da hannu a cikin kisan tare da tsananta bincike don gano su.

'Yan Sanda Sun Cafke Masu Garkuwa 7 A Bauchi

A wani labarin, rundunar 'yan sanda a jihar Bauchi ta cafke wasu da ake zargin masu garkuwa ne.

An kama wadanda ake zargin ne su bakwai a karamar hukumar Alkaleri da ke jihar kamar yadda SP Ahmed Wakili, kakakin rundunar ya tabbatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.