“Ta Yi Kama Da Mutum”: Matashi Da Ya Gaza Samun Budurwa Ya Siya Mutum-Mutumi a Bidiyo

“Ta Yi Kama Da Mutum”: Matashi Da Ya Gaza Samun Budurwa Ya Siya Mutum-Mutumi a Bidiyo

  • Wani matashi ya garzaya soshiyal midiya don baje kolin mutum-mutumi da ya barowa kansa saboda ya gaza samun budurwa
  • Mutumin ya nuna yadda ya ciro mutum-mutin daga kwalinta sannan ya dunga motsa jikinta da taimakon wani rimot
  • Wasu maza sun nuna sha'awarsu na son mallakar irin mutum-mutuminsa, yayin da wasu suka ce ta yi kama da mutum

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani mutumi ya baje kolin mutum-mutuminsa a soshiyal midiya, yana mai cewa ya siye ta saboda ya gaza samun budurwa mutum.

A wani bidiyon TikTok, mutumin ya fito da mutum-mutuminsa mai tsawon mutum daga cikin kwali sannan ya dungi motsa jikinta da taimakon na'urar da ta zo da shi.

Saurayi ya siya mutum-mutumi saboda ya gaza samun budurwa
“Ta Yi Kama Da Mutum”: Matashi Da Ya Gaza Samun Budurwa Ya Siya Mutum-Mutumi a Bidiyo Hoto: Portia, TikTok/@bradtnfi6ol
Asali: Getty Images

Ya tambayi masu kallonsa game da ra'ayinsu a kan sabuwar budurwarsa. Bidiyonsa ya burge masu kallo fiye da miliyan shida a TikTok a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Saurayi Ya Hana Budurwa Shiga Gidansa Bayan Ta Kai Masa Ziyarar Bazata, Ya Mata Bidiyo

Mutane sun yi tunanin cewa ta yi kama da mutum sannan suka yi al'ajabin abubuwan da za ta iya yi. Sai dai kuma, wadanda suke son samawa kansu irinta sun bayyana masa ra'ayinsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Robert Hocker ya ce:

"Shin tana girki?....lol"

user4987644233395 ya ce:

"Lol. Nima ina son daya. A ina zan yi oda?"

mohammed_daterush ya ce:

"A kalla dai wannan ba za ta tambayeka kudi ba."

sikayenaedna ya ce:

"Ni kadai ne na yi tunanin mutum ce."

abassquansah ya ce:

"A kodayaushe zan zabi wannan sama da kudin sadaki."

Born_star ya ce:

"Fada mana gaskiya menene dalilin da yasa ka siya mutum-mutumin."

Mr. Scanty GH ya ce:

"Shakka babu zan bukaci guda daya. Babu budurwa. Za ta yi mun daidai."

Wani mutum ya cika burinsa na son zama tamkar dabba, ya zama kare

Kara karanta wannan

“Miliyan 4 Aka Biya Ni”: Matashi Da Ya Rikide Ya Koma Mace Ya Yi Tafiyar Rangwada Da Takalma Masu Tsini, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

A wani labari na daban, wani ya cire tsabar kudi fiye da naira miliyan 10 domin ganin mafarkinsa na son zama kare ya zama gaskiya.

A cewar mutumin dan kasar Japan mai suna Toco tun yana da karamin yaro yake da burin son ganin ya zama tamkar wani dabba musamman ma ace ga shi yau ya zama tamkar wani kare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng