Wata Uwa Ta Koma Kula Da Mutum-mutumi Saboda Diyarta Mai Shekaru 21 Ta Ki Haifa Mata Jika

Wata Uwa Ta Koma Kula Da Mutum-mutumi Saboda Diyarta Mai Shekaru 21 Ta Ki Haifa Mata Jika

  • Wata matashiya ta nuna abun ban dariya da mahaifiyarta ta yi saboda bata haifa mata dan jikkale ba
  • Mahaifiyar tata wacce ta matsu ta nemo mutum-mutumi sannan take bashi kulawa tamkar dan gaske, lamarin da ya ba matashiyar mamaki
  • Bidiyon mahaifiyarta tana kula da dan mutum-mutumin ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya yayin da mutane suka bayyana ra’ayinsu

Wata matashiyar budurwa ta garzaya soshiyal midiya don wallafa wani bidiyo na mahaifiyarta da ke nunawa dan mutum-mutumi da ta siya gata.

A cewar matashiyar, mahaifiyarta wacce ta matsu ta yanke shawarar samo mutum-mutumi saboda ta ki ta haifa mata jika.

Mace da mutum-mutumi
Wata Uwa Ta Koma Kula Da Mutum-mutumi Saboda Diyarta Mai Shekaru 21 Ta Ki Haifa Mata Jika Hoto : TikTok/@monieee.b
Asali: UGC

A wani bidiyo da ya yadu a TikTok, an gano mahaifiyar tata tana shirya wani dan mutum-mutumi tamkar dan gaske kuma ta yi biris da diyar tata wacce ke daukar bidiyonsu.

Kara karanta wannan

Miji Nagari: 'Dan Najeriya ya ba Matarsa Kyautar Adaidaita Sahu 2 Ranar Zagayowar Haihuwarta

Da take bayanin bidiyon, matashiyar ta dauki abun da mahaifiyar tata take a matsayin abun dariya, tana mai cewa shekarunta 21 kacal a duniya kuma ba ta tare da kowani namiji.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta ba mahaifiyarta hakuri, cewa ita din yarinya ce karama har yanzu. Ta rubuta a bidiyon:

"Yi hakuri hajiya, ni karamar yarinya ce kuma ina farin ciki."

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

arieslovexx ta ce:

"Kuma kada ki bari wani ya matsa maki ki haifi da har sai kin shirya dari bisa dari sannan ki nemawa dan uba nagari."

K.DRAMA-queen ta ce:

"Aww hakan ya yi kyau. mahaifiyata bata ga nata jikan ba har yanzu. shekaru shida kenan da aka haife shi mun yi nesa sosai da juna."

Sarah ta ce:

"Saboda idan aka zo kan batun rainon jikan da ake magana a kai ne za su ce "na rigada na gana rainon nawa 'ya'yan."

Kara karanta wannan

Daga Yanzu Na Daina Zage-zage a Soshiyal Midiya, Murja Ibrahim Kunya

Pearledbluntsss ta ce:

"A'a kada ki yi mun zancen jika sai dai idan za ki kula da su na kwanaki 5 a mako daya."

Yan sanda sun gurfanar da ango saboda ya kara aure

A wani labari na daban, mun ji cewa rundunar yan sanda a jihar Lagas ta gurfanar da wani magidanci bisa zarginsa da kara aure a kan aure da kuma bayar da bayanan karya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel