Bincike Ya Tabbatar Cewa Yin Taku 4,000 A Rana Zai Rage Saurin Mutuwa Ga Dan Adam
- Binciken masana lafiya sun bayyana cewa takun da ya kai dubu hudu a rana na rage saurin mutuwa na dan Adam
- Ana bukatar masu shekaru 60 zuwa sama a kullum su rinka taku dubu shida zuwa 10 don kaucewa mutuwar wuri da kashi 42
- Yayin da masu shekaru kasa da 60 ake bukatar taku dubu bakwai zuwa 13 don samun raguwar da kashi 49
Sabon bincike ya tabbatar da cewa takun da ya kai dubu 4 akalla za su yi matukar tasiri wurin rage barazanar mutuwa da wuri.
Binciken ya kuma tabbatar da cewa taku akalla 2,337 a rana ka iya rage barazanar mutuwa ga dan Adam musamman cututtukan da su ka shafi zuciya.
Mujallar Kiyaye Cututtukan Zuciya na Nahiyar Turai a ranar Laraba 9 ga watan Agusta ta an yi binciken ne daga mutane 227,000 daga Australia da Amurka da Burtaniya da Spain da kuma Japan.
Masu binciken sun tabbatar cewa taku akalla dubu hudu a rana na da matukar tasiri ga lafiyar mutane da al'umma baki daya, TheCable ta tattaro.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Binciken ya kara da cewa akwai bukatar mutane su rinka taku a ko wace rana saboda amfanin hakan ga lafiyar kwakwalwarsu da jininsu baki daya.
Taku nawa ake bukata daga dattawa?
Manyan mutane da suka kai shekaru 60 zuwa sama da suka yi tafiya taku dubu shida zuwa 10 sun samu ragin kashi 42 na mutuwa da wuri.
Yayin da mutane kasa da shekaru 60 da su ka yi taku dubu bakwai zuwa 13 sun samu ragin kashi 49 daga mutuwa da wuri.
Wa ya yi wannan bayanin?
Mataimakin editan hukumar kula da cututtukan zuciya na Nahiyar Turai, Maciej Banach ya ce yawan takunka a rana yawan karuwar lafiyarka.
Ya ce:
"Yawan kara taku daga dari biyar zuwa dubu daya na kara rage yawan mutuwa na mutane."
Binciken ya ce duk wani taku a rana da bai kai dubu biyar ba, ana daukan hakan kamar zaman wuri daya ne kawai.
Lokutan Da Ya Kamata A Yi Jima'a
A wan labarin, an bayyana lokutan da ma'aurata ya kamata su na jima'ai idan suna son karuwar dankon soyayya.
Kamfanin kula da kiyon lafiya a Burtaniya, wanda kwararrun masu binciken lafiya Andy Duckworth da Paul Finnegan suka kafa a 2019 ne suka bayyana haka.
Asali: Legit.ng