Sojin Jamhuriyar Nijar Sun Kafa Sabuwar Gwamnati Mai Minitoci 21

Sojin Jamhuriyar Nijar Sun Kafa Sabuwar Gwamnati Mai Minitoci 21

  • Shugaban sojin mulki na Jamhuriyar Nijar, Abdourahamane Tchiani ya kafa sabuwar gwamnati mai dauke da ministoci 21
  • Tchiani ya bayyana haka ne a jiya Laraba 9 ga watan Agusta da dare ta kafar talabijin na kasar don tabbatar da ikonsu
  • Wannan na zuwa ne yayin da kasar ke fuskantar barazana daga kasashe musamman na Yammacin Afirka, ECOWAS

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Yamai, Nijar – Shugaban sojin Jamhuriyar Nijar, Abdourahamane Tchiani ya kafa sabuwar gwamnati mai dauke da ministoci 21 a kasar.

Tchiani ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ta kafar talabijin a ranar Laraba 9 ga watan Agusta da dare.

Sojin Nijar sun kafa sabuwar gwamnati mai dauke da ministoci 21
Shugaban Sojin Jamhuriyar Nijar, Abdourahamane Tchiani Ya Sanar Da Nadin Minitoci. Hoto: BBC.
Asali: Getty Images

Sojojin juyin mulkin sun nada ministoci 21 don kara tabbatar da ikonsu a kasar yayin da su ke fuskantar barazana daga wasu kasashe.

Yaushe ECOWAS za ta sake ganawa?

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin da Tsohon Shugaban Yan Tawayen Nijar Ya Kaddamar Da Wata Kungiya Don Yakar Masu Juyin Mulki

Tchiani ya ce sabon Fira Minista Ali Mahaman Zeine Lamine shi zai jagoranci gwamnatin mai mambobi 21 daga jiya Laraba, Vanguard ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin sabbin minstocin akwai na tsaro da na cikin gida guda biyu don sabuwar rundunar zartarwa na sojojin kasar.

Wannan na zuwa yayin da Kungiyar Raya Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ke shirin yin wata ganawa a yau Alhamis 1 ga watan Agusta a birnin Tarayyar Najeriya, Abuja, TRT Afirka ta tattaro.

Har ila yau, sojojin na zargin kasar Faransa da sake wasu masu ikirarin jihadi ganin yadda hakan ya saba dokar da suka kafa na rufe sararin samaniyar kasar.

Me sojojin ke zargin Faransa a kai?

Sojojin su ka ce Faransa ta sake masu jihadin ne da su ka dade a tsare wanda saba doka ce hakan da cewa Faransa ta yi gaban kanta wurin keta musu dokoki.

Kara karanta wannan

Tsohon Sarkin Kano Sanusi II Ya Zauna Da Sojojin Da Suka Kifar Da Bazoum a Nijar

Kungiyar ECOWAS ta gargadi sojin kasar da su mika mulki ga Bazoum ko su dauki tsauraran matakai a kan haka.

Wa’adin da kungiyar ta bayar ya ciki kwanaki hudu da suka wuce, ba a sani ba watakila taron na yau na da alaka da cikan wa’adin na ECOWAS.

Nijar Ta Nada Sabon Fira Minista

A wani labarin, sojojin Jamhuriyar Nijar sun nada sabon Fira Minista, Ali Mahama Lamine don gudanar da harkokin gwamnati.

Mahaman tsohon ma'aikacin Bankin Raya Afrika (AfDB) ne kuma tsohon ministan kudi a lokacin Mamadou Tandja da aka kifar a 2010.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.