Kotun Zabe: Mary Odili Tana Aiki Domin Tinubu Ya Samu Nasara? Gaskiya Ta Fito
- Mai shari'a Mary Ukaego Peter-Odili ta fusata kan batun da wani mai suna Jackson Ude ya yi a soshiyal midiya cewa tana yi wa Tinubu aiki don yin nasara a kotun zaɓe
- Ude ya kuma yi iƙirarin mai shari'a Odili tana ganawa sosai da alƙalan kotun ɗaukaka ƙara da kotun ƙoli akan lamarin
- Mai shari'ar kotun ƙolin wacce ta yi murabus, ta fitar da sanarwa a ranar Laraba, 9 ga watan Agusta, inda ta nuna ɓacin ranta kan wannan zargin
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Mary Peter-Odili, alƙaliyar kotun ƙoli wacce ta yi murabus, ta musanta zargin nuna son kai da cin hanci da ake mata.
Maganganu sun yi yawa a soshiyal midiya cewa Mrs Odili tana aiki tare da alƙalan kotun ɗaukaka ƙara domin tabbatar da cewa Shugaba Tinubu ya yi nasara akan ƙarar da jam'iyyun adawa suka shigar ta ƙalubalantar nasararsa a zaɓe.
'Ƙarya ce kawai', Odili ta fusata kan zargin
Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jami'iyyar Labour Party (LP), da Alhaji Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), suna ƙalubalantar sakamakon zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu wanda Shugaba Tinubu ya lashe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani mai amfani da sunan Jackson Ude a Twitter, ya yi zargin cewa Peter-Odili tana taimakawa Shugaba Tinubu ya samu hukuncin da zai yi masa daɗi a kotun zaɓen.
Ude shi ne kuma ya zargi tsohon gwamnan jihar Legas, Babatunde Fashola, da rubuta hukuncin kotun zaɓe, wanda hakan ya sanya tsohon ministan kai ƙara gaban babban sufetan ƴan sanda, Egbetokun Olukayode.
Da take martani kan zargin cikin wata sanarwa da kakakinta Felix Enebeli, ya fitar, Odili ta bayyana zargin a matsayin ƙarya ce tsagwaronta, cewar rahoton The Cable.
Yanzu-Yanzu: ECOWAS Ta Sake Sanya Sabbin Takunkunmi Kan Juyin Mulkin Jamhuriyar Nijar, Bayanai Sun Fito
Wani rahoton jaridar Leadership na ranar Alhamis, 10 ga watan Agusta, ya nuna martanin da Odili ta yi.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Mun musanta dukkanin zarge-zargen da aka yi, sannan zargin ƙarya ce tsagwaronta wacce aka yi da gangan domin ɓata suna da dattakon mai shari'a Odili."
Haka kuma, Enebeli ya bayyana cewa lauyoyin Odili na aiki kan lamarin inda suka buƙaci Ude ya janye kalamansa tare da neman afuwa.
Mai Shari'a Ya Musanta Yin Murabus
A wani labarin kuma, mai shari'a Boloukourom Ugo ya musanta zargin cewa ya yi murabus daga zama cikin alƙalan dake sauraron ƙarar zaɓen shugaban ƙasa.
Kotun ɗaukaka ƙara ita ce da kanta ta fito ta musanta batun murabus ɗin mai shari'a Ugo, bayan batun ya karaɗe shafukan sada zumunta.
Asali: Legit.ng