Abdullahi Ganduje Ya Gyara Zama a APC, Ya Yi Nadin Mukami Daga Shiga Ofis

Abdullahi Ganduje Ya Gyara Zama a APC, Ya Yi Nadin Mukami Daga Shiga Ofis

  • Malam Muhammad Garba ya bi Dr. Abdullahi Umar Ganduje bayan zama shugaban APC
  • ‘Dan jaridan ya kasance Kwamishinan labarai a Kano kuma tun 1999 yake tare da Dr. Ganduje
  • Bayan zamansa Kwamishina, Garba ne Kakakin kwamitin yakin zaben Gawuna/Garo

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya nada wanda zai zama shugaban ma’aikata a ofishinsa.

Premium Times ta ce Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya tafi da Malam Muhammad Garba a matsayin shugaban ma’aikatansa a APC.

Kafin yanzu Muhammad Garba ya kasance Kwamishinan yada labarai a lokacin da Dr. Abdullahi Ganduje ya yi Gwamna a jihar Kano.

Abdullahi Ganduje
Abdullahi Ganduje ya jagoranci taron APC NWC Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

Jam'iyyar APC ta fitar da sanarwa

Darektan yada labarai na jam’iyyar APC, Bala Ibrahim ya sanar da nadin Malam Garba a Abuja. Garba ya samu digiri biyu daga jami’ar BUK.

Kara karanta wannan

Sanusi II Ya Yi Maganar Farko Bayan Haduwa da Tinubu da Sojojin Juyin Mulkin Nijar

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tsohon shugaban kungiyar ‘yan jarida na kasan (NUJ) ya taba kasancewa Kwamishinan labarai, matasa, wasanni, al’adu da tsaron gida.

Aiki da gwamnatoci a Najeriya

Kafin zama kwamishina, Garba ya yi babban kwamishina daga shekarar 2011 har zuwa 2014 a FRC, jaridar ta ce kungiyoyi sun yaba da nadinsa.

‘Dan siyasar ya yi aiki na shekaru uku a hukumar SURE-P da aka kirkira bayan cire tallafin mai, kuma shi ne kakakin APC a Kano a zaben 2023.

Mukaman da ya rike kafin zuwan APC

A fagen aikin jarida, sabon hadimin shugaban jam’iyyar APC ya yi shugabancin NUJ sau biyu, sannan ya taba zama shugaban kungiyar WAJA.

WAJA ita ce kungiyar ‘yan jarida ta yammacin Afrika, Garba ya jagorance ta a baya.

The Nation ta ce Garba ya taba lashe zabe ya zama shugaban kungiyar FAJ ta Afrika kafin ya shiga kwamitin kungiyar IFJ ta Duniya a Dublin.

Kara karanta wannan

Ganduje: ‘Dan Takarar Shugaban Kasa a PDP Ya Yi Ƙus-Ƙus da Sabon Shugaban APC

A 1993 ya yi sakataren yada labarai ga mataimakin shugaban majalisar wakilai, ya maimaita kujerar daga 1999 zuwa 2003 a gwamnatin Kano.

Mariya Bunkure/Maryam Shetty

Ku na da labari siyasar Kano ta na daukar wani fasali na dabam bayan Bola Ahmed Tinubu ya dare kan mulki yayin da NNPP ta karbe Jihar.

Ana haka sai aka ji bidiyo ya tona Abdullahi Ganduje da mai dakinsa da wasu mata su na gulmar Maryam Shetty wanda ta ga samu da rashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng