“NPC Ta Shirya Gudanar Da Kidaya, Umarnin Tinubu Kawai Muke Jira”, In Ji Kwamishinan Tarayya

“NPC Ta Shirya Gudanar Da Kidaya, Umarnin Tinubu Kawai Muke Jira”, In Ji Kwamishinan Tarayya

  • Hukumar Kidaya ta Kasa ta ce umarnin Shugaba Bola Tinubu kawai take jira ta fara aikinta
  • Kwamishinan hukumar na tarayya, Clifford Zirra ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai
  • Ya ce hukumar ta gama tanadar duk wani abinda ya kamata don fara gudanar da aikin ƙidayar na 2023

Yola, Adamawa - Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC), ta ce ta tanadi duk abinda ya kamata domin gudanar da ƙidayar jama’a da gidaje na shekarar 2023.

Kwamishinan tarayya na NPC a Adamawa Clifford Zirra ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Yola babban birnin jihar kamar yadda PM News ta wallafa.

NPC ta ce tana jiran umarnin Tinubu
Hukumar Kidaya ta Kasa ta ce umarnin Tinubu kawai suke jira. Hoto: National Population Commission
Asali: Facebook

Abinda Hukumar Kidaya ta Kasa ke jira

Zirra ya bayyana cewa hukumar na jiran umarnin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne kawai domin fara aikinta.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Jigon PDP Ya Faɗawa ECOWAS Muhimman Abubuwa 9 Da Ya Kamata Su Sani a Kan Sojojin Nijar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu ya gamsu matuƙa da abubuwan da hukumar ta cimmawa ya zuwa yanzu.

Ya ce ƙidayar za ta taimaka wajen matuƙa wajen sauya fasalin al'amura a Najeriya, saboda za ta bai wa shugabannin damar aiwatar da tsare-tsare wajen gudanar da ayyukansu ga 'yan ƙasa.

Muhimmancin ɗaga aikin ƙidayar da aka yi a baya

Zirra ya kuma yaba da matakin ɗage ƙidayar da Gwamnatin Tarayya ta ɗauka a wancan lokacin na ɗage aikin ƙidayar zuwa gaba.

Ya ce hakan ya bai wa sabuwar gwamnati damar yin nazari kan ayyukan hukumar, da kuma sanin yadda za a gudanar da aikin kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.

Ya ƙara da cewa ɗagawar da aka yi ta bai wa ita kanta hukumar damar ƙara shiryawa musamman ma da ya kasance wannan ne karo na farko da za a gudanar da aikin ƙidaya ta amfani da manhajoji na zamani.

Kara karanta wannan

"Shugaba Tinubu Ya Fi Sauran Shugabannin Najeriya", Cewar Jigon APC, Ya Bayyana Kwakkwaran Dalili

Yanzu dai hukumar na jiran umarnin shugaba Tinubu ne wajen tsaida sabuwar ranar da za ta fara gudanar da aikin ƙidayar.

An buƙaci shugaban Majalisar Dattawa ya yi murabus

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan ɓaranɓaramar rabon kuɗi da shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio ya yi a yayin da ake gudanar da zaman majalisar.

Hakan ya janyo masa suka daga 'yan Najeriya da dama, inda wasu daga cikinsu suka buƙaci ya yi murabus daga kan kujerarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng