Cire Tallafin Mai: Gwamnan Najeriya Ya Sanar Da Shirin Tallafi Ga Ma’aikata Da Dalibai

Cire Tallafin Mai: Gwamnan Najeriya Ya Sanar Da Shirin Tallafi Ga Ma’aikata Da Dalibai

  • Gwamnatin jihar Ekiti ta sanar da wasu matakan tallafi da ta tanada don ragewa al’ummarta radadin cire tallafin man fetur
  • Gwamna Biodun Oyebanji ya sanar da shirin samar da motocin kyauta ga ma’aikata da dalibai da kuma biyan alawus duk wata
  • Oyebanji ya kuma sanar da biyan N5,000 a matsayin tallafi ga iyalai 10,000 daga watan Agusta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ekiti - Gwamna Biodun Oyebanji na jihar Ekiti ya sanar da wasu matakan tallafi ga ma'aikata da dalibai a jihar don rage masu radadin cire tallafin man fetur.

Oyebanji ya sanar da tanadinsu na samar da motocin kyauta ga ma'aikata da dalibai da kuma biyan alawus ga wasu iyalai duk wata, jaridar Vanguard ta rahoto.

Gwamna Biodun Oyebanji
Cire Tallafin Mai: Gwamnan Najeriya Ya Sanar Da Shirin Tallafi Ga Ma’aikata Da Dalibai Hoto: @biodunaoyebanji
Asali: Twitter

Za a samar da motocin kyauta ga ma'aikata da dalibai a Ekiti

Kara karanta wannan

Bidiyon Akpabio Yana Sanar Da Cewa An Tura Wa Yan Majalisa Kudaden Shakatawa Yayin Hutu Ya Janyo Cece-Kuce

Kwamishinan kudi, Akintunde Oyebode, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya mikawa manema labarai a Ado-Ekiti a ranar Laraba, 9 ga watan Agusta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar sanarwar, tallafin sun hada da:

“Biyan bashin fansho na wata daya ga yan fansho na jiha da na kananan hukumomi.
"Aiwatar da gyare-gyare ga ma'aikata a matakin GL. 14 zuwa GL. 17 a matakin Jiha da Kananan Hukumomi.
“Aiwatar da shirin biyan alawus ga ma’aikatan lafiya a kananan Hukumomi.
“Aiwatar da daidaiton albashi ga ma’aikatan asibiti na Hukumar Kula da Asibitoci.
“Aiwatar da shirin cin gajiyar kudi na 2020 da karin matsayi na 2021 ga ma'aikatan Jiha da Kananan Hukumomi.
"Gaggauta biyan bashin da manyan makarantu ke bi na wata daya.
"Samar da motocin kyauta ga ma'aikata da dalibai domin saukaka zirga-zirga zuwa wajen aiki da dawowa da kuma zuwa makaranta da dawowa.

Kara karanta wannan

Sunayen Ministocin Tinubu 2 Da Aka Tabbatar Duk Da Suna Da Wata Babbar Matsala a Tattare Da Su

"Biyan N5,000 ga iyalai 10,000 daga watan Agusta har zuwa Disambar 2023, wanda zai ta'allaka kan tsoffinmu.
"Sanya mutum 10,000 a shirin inshoran lafiya na Ulera Wa.
"Shirin raba abinci da zai fara aiki a watan nan.
"Rabon kayan aiki ga manoma da kuma tallafin kudi ga kananan 'yan kasuwa da masu siyar da abubuwan amfani na yau da kullun."

Tinubu ya gana da majalisar koli ta shari'a

A wani labarin kuma, mun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ganawar sirri da mambobin majalisar koli ta shari'a a Najeriya a ranar Laraba, 9 ga watan Agusta.

Ba a bayyana cikakken bayanin ganawarsu va amma Legit.ng ta fahimci cewa wannan shine karo na farko da malaman Musuluncin ke ganawa da Tinubu tun bayan da ya hau karagar mulki a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng