Gwamnan Jihar Adamawa Ya Amince Da Bayar Da Tallafin N10,000 Ga Ma'aikata Da 'Yan Fansho

Gwamnan Jihar Adamawa Ya Amince Da Bayar Da Tallafin N10,000 Ga Ma'aikata Da 'Yan Fansho

  • Gwamnan jihar Adamawa ya tuna da ma'aikata da ƴan fansho a jihar a lokacin da ake ci gaba da shan raɗaɗin cire tallafin man fetur
  • Gwamna Fintiri ya amince da tallafin N10,000 ga ma'aikata da ƴan fansho a jihar wanda za a riƙa bayarwa har na tsawon wata shida
  • Gwamnatin jihar za ta kuma siyo masara da shinkafa domin rabawa al'ummar jihar akan farashi mai rahusa

Jihar Adamawa - Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya amince da tallafin N10,000 duk wata ga ma'aikata da ƴan fansho a jihar domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa za a bayar da tallafin ne har na tsawon wata shida.

Gwamnan jihar Adamawa ya ba da tallafin N10,000 ga ma'aikata
Gwamnatin ta bayar da tallafin domin rage radadin cire tallafin man fetur Hoto: Gov Ahmadu Umaru Fintiri
Asali: Facebook

Shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar wanda shi ne shugaban kwamitin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur na jihar, Dr Edgar Amos, shi ne ya bayyana hakan ga manema a labarai ranar Laraba a fadar gwamnatin jihar dake birnin Yola.

Kara karanta wannan

Da Dumi-ɗumi: Allahu Akbar, An Gano Jaririn da Aka Sace a Babbar Kasuwar Arewacin Najeriya

Ya kuma bayyana cewa gwamnan ya amince a riƙa biyan ma'aikatan ƙananan hukumomi mafi ƙarancin albashi daga albashin wata mai kamawa, rahoton The Nation ya tabbatar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnatin za ta yi wa al'ummar jihar rabon kayan abinci

Dr Edgas Amos ya ci gaba da cewa gwamnnatin jihar za ta siyo manyan motoci na masara guda 70 da manyan motoci na shinkafa guda 20 domin rabawa jama'a akan farashi mai rahusa.

Ya kuma ƙara da cewa gwamnatin za ta siyo manyan motoci 50 na taki domin siyarwa ma'aikata akan farashi mai rahusa, tare da siyo ƙananan motoci domin jigilar ma'aikatan.

Shugaban ƙungiyar ma'aikata a jihar, Dauda Adamu Aliyu, ya bayyana cewa matakan da gwamnatin ta ɗauka abun a yaba ne domin za su taimaka wajen rage raɗaɗin da ake fama da shi.

Ma'aikatan Kwara Da Ogun Za Su Dara

Kara karanta wannan

Cire Tallafin Man Fetur: Gwamnonin APC 2 Sun Amince Da Rabon Tallafin N10,000 Ga Ma'aikata

A wani labarin kuma, gwamnonin jihohin Kwara da Ogun sun amince da biyan tallafin N10,000 ga ma'aikata a jihohinsu domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Gwamna Abiodun na jihar Ogun ya kuma amince da biyan kuɗaɗen alawus na ma'aikatan lafiya a faɗin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng