Kotu Ta Daure Ya Da Kanwa Watanni 18 A Gidan Kaso Kan Zargin Satar Man Goge Baki A Ogun
- Kotun majistare da ke Abeokuta ta gurfanar da wasu mata ya da kanwa kan zargin satar man goge baki a jihar Ogun
- Wadanda ake zargin Gbenga da Funmilayo Elegbede sun fasa shago da kuma gidan wasu mutane tare da yin sata
- Da ya ke yanke hukunci, mai shari’a E. Idowu ya daure Gbenga na tsawon shekara daya yayin da Funmilayo aka yanke mata watanni shida
Jihar Ogun – Kotun majistare da ke zamanta a jihar Ogun ta daure ya da kanwa, Gbenga Elegbede da Funmilayo Elegbede watanni 18 a gidan kaso.
Ana zargin ‘yan uwan da satar man goge hakori da satar kaya na wasu mutane biyu, Alhaji Wahab da Adeleke Omolayo.
Wane irin hukunci aka yanke a kotun?
Yayin yanke hukunci, mai shari’a E. O Idowu ya daure Gbenga na tsawon shekara daya da aiki mai wahala yayin Funmilayo aka yanke mata zaman watanni shida da aikin wahala, cewar Punch.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An yanke hukuncin ne a ranar Laraba 9 ga watan Agusta bayan dukkan wadanda ake zargin sun tabbatar da aikata laifukan da ake tuhumarsu.
Mai gabatar da kara, Laide Rawlings ta fadawa kotu cewar ‘yan uwan junan sun balla shagon Adeleke Omolayo tare da satar kaya da su ka kai N291,150 da suka hada da silifas da man goge baki uku da tabarma da tukunyar Gas.
Ta kara da cewa ‘yan uwan sun kuma fasa gidan Alhaji Wahab tare da satar jakar kudi karama da ke dauke da Naira dubu 450,000, Head Topics ta tattaro.
Me lauyar wadanda ake zargi ta ce wa kotu?
Rawlings ta ce aikata hakan ya sabawa kundin tsarin mulki sashe na 127,390 da sashe na 516 na kundin laifuffuka da hukunci na jihar Ogun.
Gbenga da Funmilayo sun amince da aikata laifukan inda su ka roki kotun ta musu sassauci ganin cewa Gbenga ta na shayar da jaiririya ‘yar wata uku.
Da ta ke martani kan hukuncin, lauyan wadanda ake zargi, Barista Nafisat Mas’ud ta bayyana hukunci da cewa an yi shi cikin adalci Anaedo Online ta tattaro.
Kotu Da Daure Wata Mata Kan Zargin Cizon Mai Kokarin Sasanta Su A Abuja
A wani labarin, kotun da ke zamanta a Abuja ta daure wata mata da ake zargin da cizon mai musu sulhu yayin da su ke fada.
Wacce ake zargin Chioma Okeke ta ciji Roseline ne a shagonta yayin da su ka kaure da fada da kwastomarta.
Asali: Legit.ng