Tawagar Majalisar Koli Ta Shari’a Ta Gana Da Shugaban Kasa Tinubu, Cikakken Bayani Ya Bayyana
- Mambobin majalisar koli ta Shari'a a Najeriya sun gana da Shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Laraba, 9 ga watan Agusta
- Shugaban kasar ya tarbi shugabannin Musuluncin a zauren fadar shugaban kasa da ke Abuja
- Koda dai ba a san cikakken dalilin ganawar tasu ba amma wannan shine karo na farko da malaman musuluncin ke ganawa da shugaban kasar tun bayan da ya hau mulki
Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ganawar sirri da mambobin majalisar koli ta shari'a a Najeriya a ranar Laraba, 9 ga watan Agusta.
Dalilin da yasa majalisar koli ta Shari'a ta ziyarci Tinubu
Kamar yadda NTA News ta rahoto, ba a bayyana cikakken bayanin ganawarsu va amma Legit.ng ta fahimci cewa wannan shine karo na farko da malaman Musuluncin ke ganawa da Tinubu tun bayan da ya hau karagar mulki a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu.
Bayanai game da majalisar koli ta shari'a
Majalisar koli ta Shari'a wata kungiya ce ta malamai da shugabannin Musulunci a Najeriya. An kafa ta ne a 1990 domin bunkasa koyarwar addinin Islama da kuma kare hakkin Musulmai a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tantance ministoci: Kada ka rantsar da El-Rufai, Malaman Musulunci sun gargadi Tinubu
Legit.ng ta rahoto a baya cewa gamayyar kungiyar makaranta da mahaddatan Al-Qur'ani sun yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu sannan sun gabatar da wani babban bukata a gabansa.
Malaman Musuluncin sun bukaci shugaban kasa Tinubu da kada ya rantsar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai a matsayin minista a majalisarsa saboda adalci, gaskiya, zaman lafiya da dorewar kasar nan.
Da yake magana da manema labarai a Bauchi a madadin malaman, daraktan kula da ilimi na gidauniyar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Sheikh Sidi Aliyu Sise, ya shawarci Tinubu da ya yi taka-tsan-tsan sannan kada ya rantsar da azalluman yan siyasa da ke da kuntun kashi a tsuliyarsu.
Ya ce zabar El-Rufai da tantance shi da majalisar dokokin tarayya ta yi rashin adalci ne ga masu karatu da masu haddar Al-Qur'ani saboda tauye su da ya yi a lokacin da yake matsayin gwamna.
Asali: Legit.ng