Kotu Da Daure Wata Mata Kan Zargin Cizon Mai Kokarin Sasanta Su A Abuja, Ta Samu Sakamako
- Kotun sauraran korafe-korafe da ke zamanta a Abuja ta tsare wata mata kan zargin cin zarafi da kuma kai hari
- Wacce ake zargin, Chioma Okeke ta kai cizo ga wata mai sulhu yayin da su ke fada a hannun dama
- Alkalin kotun, Mallam Muhammad Wakili ya umarci wacce ake zargin ta biya kudin beli Naira dubu 500
FCT, Abuja - An gurfanar da wata mata mai suna Chioma Okeke a kotun da ke zamanta a Kado da ke birnin Tarayya Abuja.
Wacce ake zargin mai shekaru 27, ana tuhumarta da cizon mai sulhunta tsakaninsu yayin da su ke fada a shagonta.
Dan sanda ya gabatar da Okeke kan zargin raunata mai kara, kamar yadda Vanguard ta tattaro.
Me wacce zargi ta fadawa kotu kan zargin?
Wacce ake zargi ta musanta tuhumarta da ake kan zargin cizo da kuma kai hari.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mai gabatar da kara, Stanley Nwafoaku ya fadawa kotu cewa Roseline Isonguyoyo ta kai karar Chioma ofishin yanki na 'yan sanda da ke Utako.
Nwafoaku ya ce wanda ake zargin ta je har wurin aikin Roseline inda su ka kaure da kwastomarta a Wuse Zone 5.
Ya kara da cewa Chioma ta naushi Roseline tare da cizon ta a hannunta na dama da kuma yaga mata riga, Naija News ta tattaro.
Ya ce Roseline ta garzaya zuwa asibiti inda ta biya N15,000 na jinya bayan Chioma ta ji mata ciwo a gefen idonta.
Wani hukunci alkalin kotun ya yanke?
Alkalin kotun, Malam Muhammad Wakili ya umarci wanda ake zargi ta biya kudin beli Naira dubu 500.
"Na Fusata Ne Kuma Ga Yunwa": Yadda Wani Bakano Ya Raunata Dan Mai Koko Saboda Ta Ki Siyar Masa Da Bashi
Ya bukaci wanda zai tsaya mata ya kawo katin shaidar aiki da hoto da kuma takardar BVN na wacce ake zargi.
Muhammad Wakili ya dage sauraran karar zuwa ranar 19 ga watan Satumba na wannan shekara.
Mata Ta Maka Mahaifyarta A Kotu Don Sanin Waye Mahaifinta A Abuja, Ta Ce Ta Gaji Da Gori
A wani labarin, wata mata ta maka mahaifiyarta a kotu don nemo mata mahaifinta duk ida ya ke.
Matar mai suna Hauwa'u Abubakar ta ce ta gaji da irin gori da kannenta ke mata kan cewa mahaifinsu ba daya ba ne.
Mahaifiyar ta aka maka a kotun daga bisani ta kawo wani mutum a matsayin mahaifin matar amma ya karyata hakan.
Asali: Legit.ng