Musulmai a Jihar Legas Sun Koka Kan Rashin Samun Gurabe a Cikin Sunayen Kwamishinoni
- Jerin sunayen da gwamnan jihar Legas ya aike zuwa gaban majalisar dokokin jihar domin tantancewa ya bar baya da ƙura
- Wata ƙungiyar musulmai a jihar ta fito fili ta caccaki jerin sunayen saboda abin da ta kira rashin adalci ga al'ummar musulmai
- Ƙungiyar ta koka kan yadda babu sunayen musulmai masu yawa a cikin jerin sunayen kwamishinonin da gwamna zai naɗa
Jihar Legas - Ana ci gaba da caccakar sunayen kwamishinonin da gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya aike zuwa gaban majalisar dokokin jihar.
Wata ƙungiyar malaman addinin musulunci a ranar Talata, 8 ga watan Yuli, ta bayyana jerin sunayen kwamishinonin a matsayin wani ci gaba kan nuna wariya da gwamnan yake yi ga al'ummar musulmai a jihar.
Sun bayyana cewa jerin sunayen kwamishinonin kwata-kwata babu adalci a cikinsa, cewar rahoton Premium Times.
Sauƙi Ya Zo: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Bayyana Mafi Karancin Albashin da Zata Ƙara Wa Ma'aikata a Najeriya
A wajen wani taron manema labarai da ƙungiyar Joint Muslims Forum (JMF) ta kira, a ƙarƙashin jagorancin Abdrahman Ahmad, ya bayyana cewa musulman jihar sun yi watsi da sunayen kwishinonin da gwamnan ya miƙa gaban majalisa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An saba tauye hakkin musulmai a Legas
Malam Ahmad wanda limami ne ya bayyana cewa gwamnan a baya ya saba yi wa musulman jihar rashin adalci ta hanyar rashin ba su muƙamai a gwamnati da ta ke musu haƙƙi.
Malam Ahmad ya bayyana cewa sunayen kwamishinonin ya ƙara tabbatar da cewa gwamnatin jihar ba ta ganin ƙimar al'ummar musulman jihar, rahoton The Guardian ya tabbatar.
Ya bayyana cewa sun sha kai koken su ga gwamnatin jihar amma ko sau ɗaya ta ƙi ta yi wani abu a kai.
A cewar ƙungiyar daga cikin sunayen mutum 39 na kwamishinonin, mutum takwas ne kawai musulamai.
"Musulmai ko kaso 20% ba su yi ba a cikin jerin sunayen, duk da cewa mu na da kaso 60% na yawan mutane da masu kaɗa ƙuri'a a jihar. Mun lura da cewa daga cikin mutum 39 da za a naɗa kwamishinoni, mutum takwas ne kaɗai musulmai." A cewar Malam Ahmad.
Wane abu gwamnan jihar ya ce a kai?
Amma gwamnan ya musanta zargin nuna wariya inda ya ce gwamnatinsa ba ta fifita wani addini akan wani ba, inda ya yi nuni da cewa cancanta ita ce madubin gwamnatinsa.
Tun da farko dai, ƴan majalisar dokokin jihar sun yi fatali da jerin sunayen inda suka cewa wasu ƙananan hukumomi ba su da wakilai a cikin jerin sunayen.
Sanwo-Olu Ya Fara Rabon Kayan Tallafi
A wani labarin kuma, gwamna Babajide Sanwo-Olu ya fara rabon kayan tallafi domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.
Gwamnan ya kuma bayar da umarnin rage kuɗin sufuri da kaso 50 cikin 100 a motocin bas mallakar gwamnatin jihar.
Asali: Legit.ng