Sanatan NNPP Zai Kashe Fiye da Naira Miliyan 20 Biyawa Dalibai Kudin Jami’a
- Rufai Hanga ya zabo dalibai da ke karatu a jami’ar Bayero da ke Kano, ya biya masu kudin karatu
- Sanatan ya dauki dawainiyarsu ne domin ganin yadda aka kara kudin makarantu jami’o’i a yanzu
- Tallafin ya shafi ‘yan asalin jihar Kano ta tsakiya da ke aji 2, 3, 4, 5 ko maimaci a jami’ar ta Bayero
Kano - Rufai Hanga ya zabi mutane 200 daga jami’ar Bayero da ke garin Kano, zai taimaka masu da kudin karatu na zangon shekarar nan.
Sanata Rufai Hanga mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa ya bayyana haka a shafinsa na Twitter bayan an kara kudin makaranta.
‘Dan majalisar yake cewa samun karatun zamani hakkin mutanen mazabarsa ne ba gata ba.
"Na bada tallafi ga dalibai 200 daga jami’ar Bayero da ke Kano a mazabar Kano ta tsakiya!
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ina cika alkawarin da na dauka na agazawa masu karamin karfi a yayin da ake cikin matsin lambar tattalin arziki a dalilin tashin kudin karatu.
Ilmi hakki ne, ba gata ba."
- Rufai Hanga
Daliban Kano masu rabo sun dace!
Muhammad Sameer Rufai Hanga, ya shaida cewa sai da aka tantance kafin a zakulo wadannan dalibai da ake ganin sun cancanci a tallafa masu.
Da yake bayani a shafin Facebook, Muhammad Rufai Hanga ya ce wadanda su ka nemi tallafin za su iya duba sunansu a cikin jerin da ya fitar.
“Alhamdulillahi yau cikin hukuncin Allah, list din dalibai na Bayero University Kano su 200 wayanda Sen Rufai Hanga ya dauki nauyin biya musu kudin makaranta ya kammala, dan haka duk wayanda akayiwa secreening sa Iya duba sunan su anan, ko kuma portal dinsu da zarar makaranta ta gama aikinta akan list din. Allah ya bada sa’a.
- Muhammad Rufai Hanga
Daliban da aka zabo sun hada da masu karantar Akanta, Ilmin lafiya, Larabci, Aikin gona, karatun manya, Ilmin shari’a da masu karatun nazarin alkaluma.
Akwai masu karanta ilmin dabbobi, addinin musulunci, Injiniya, tattalin arziki, tarihi, da aikin jarida.
Yadda Sanata ya zakulo mutum 200
Akwai mutane 9 daga Dawakin Kudu, 20 daga Dala, sai dalibai 10 daga mazabun Fagge, akwai kimanin 10 a Garun Malam da kusan 10 daga Gezawa.
A jerin Legit.ng Hausa ta akalla mutum 13 daga Gwale, 15 daga birnin Kano, 21 a yanin Kumbotso, sai 10 Kura da kusan 10 a Madobi da kuma Minjibir.
Baya ga wasu 18 ‘Yan Nasarawa, akwai 17 daga Tarauni sai ragowar 20 daga Warawa da Ungogo.
Abin da mutane su ke fada a kan Hanga
Hakan ya jawowa Sanatan yabo daga masu amfani da shafin Twitter. Irinsu Hameed A. Akande su na ganin Hanga ya bi tafarkin Kwankwasiyya a Kano.
Shi kuma wani @Jagabanolu ya na ganin ya kamata a hada da sauran kabilu kamar Ibo, Tibi da Kanuri da ke zama a yankin ko da ba nan ne asalinsu ba.
Munzali Ya'u gumel ya ce: “Allah ya saka maka da alheri”
Asali: Legit.ng