Juyin Mulkin Nijar: IGP Ya Umarci Manyan Jami'an 'Yan Sanda Na Jihohin Da Ke Kan Iyaka Su Tsaurara Tsaro
- Babban sufeton 'yan sandan Najeriya na riƙon ƙwarya, ya buƙaci jami'ansu su tsaurara tsaro kan iyakoki
- Olukayode Egbetokun, ya buƙaci jami'an 'yan sandan da su haɗa gwiwa da sauran jami'ai don tabbatar da tsaro
- Ya ce rundunar 'yan sandan Najeriya za ta ci gaba da sanya idanu a yankunan da aka rufe iyakokin Najeriya da Nijar
Abuja - Babban sufeton 'yan sanda na wucin gadi Olukayode Adeolu Egbetokun, ya bai wa kwamishinoni da manyan jami'an 'yan sanda na jihohin da suka yi iyaka da Nijar sabon umarni.
Ya nemi jami'an su haɗa kai da sauran jami'an tsaro domin tabbatar da cewa ba a samu wata matsala ta tsaro ba biyo bayan rufe iyakokin Najeriya da Nijar da aka yi kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Juyin Mulkin Nijar: Muhimman Abubuwa 12 Da Suka Faru Tun Lokacin Da Sojoji Suka Kifar Da Gwamnatin Bazoum
Jami'an 'yan sanda za su ci gaba da sanya idanu kan iyakokin
Egbetokun ya bayyana hakan ne a yayin wani taro na wata-wata da hukumar ke shiryawa kan harkokin tsaro da tsare-tsare kan harkokin tsaro.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce rundunar 'yan sandan Najeriya za ta ci gaba da sanya idanu a yankunan da rufe iyakokin ya shafa, don tabbatar da tsaro da lafiyar al'ummar yankin.
Jihohi bakwai ne dai daga Arewacin Najeriya suka haɗa iyakoki da jamhuriyar Nijar.
Jihohin su ne Kebbi, Sokoto, Zamfara, Katsina, Jigawa, Yobe da Borno, waɗanda aka kulle biyo bayan umarnin ƙungiyar ECOWAS.
IGP ya dakatar da ba da lasisin bindiga da 'yan sanda ke yi
Sufeton 'yan sandan ya kuma dakatar da 'yan sandan Najeriya daga ba da lasisin mallakar bindigu da akan bai wa mutane a baya.
Ya ce matakin ya zama dole ne musamman ma in aka yi la'akari da yadda ake ƙara samun yawaitar ƙananun makamai a hannun al'umma kamar yadda Blueprint ta wallafa.
Ya ce hakan ba ƙaramin haɗari ba ne ga Najeriya, duk da dai cewa al'umma na yin amfani da bindigun domin bai wa kawunansu kariya daga hare-haren 'yan ta'adda.
Sojojin Nijar sun kulle sararin samaniyar ƙasar
Legit.ng a baya ta kawo rahoto kan matakin rufe sararin samaniya da sojojin juyin mulkin jamhuriyar Nijar suka ɗauka.
Sojojin dai sun sanar da wannan matakin ne biyo bayan cikar wa'adin da ƙungiyar ECOWAS ta ba su na su miƙa mulki ga farar hula.
Asali: Legit.ng