Likitoci Sun Yi Amai Sun Lashe, Sun Janye Gudanar Da Zanga-Zangar Da Suka Shirya
- Likitoci masu neman ƙwarewa sun sanar da dakatar da zanga-zangar gama gari da suka shirya, inda suka ƙara da cewa za su yi duba kan lamarin nan da sa'o'i 72
- Emeka Orji, shugaban ƙungiyar NARD, shi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, inda ya ƙara da cewa sun cimma matsaya ne bayan ganawa da shugaban majalisar dattawa
- Tun da farko shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yi nuni da za a dakatar da zanga-zangar bayan ya gana da likitocin a ranar Talata
FCT, Abuja - Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa (NARD) sun sanar da dakatar da zanga-zangar da suka shirya a faɗin ƙasar nan bayam sun sanya labule da shugabannin majalisar dattawa a ranar Talata, 8 ga watan Agusta.
A cewar rahoton Premium Times, shugaban ƙungiyar Emeka Orji, shi ne ya tabbatar da hakan da safiyar ranar Laraba, 9 ga watan Agusta.
Juyin Mulkin Nijar: Muhimman Abubuwa 12 Da Suka Faru Tun Lokacin Da Sojoji Suka Kifar Da Gwamnatin Bazoum
Dalilin da ya sanya muka dakatar da zanga-zanga, likitoci sun magantu
A ranar Talata, wata sanarwa daga ofishin shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ta yi nuni da likitocin za su dakatar da yajin aikin bayan ganawar da suka yi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Orji a cikin wata tattaunawa ta wayar tarho da safiyar ranar Laraba ya tabbatar da cewa ƙungiyar ta dakatar da zanga-zangar da ta shirya gudanarwa yau (Laraba), sannan ƴan Najeriya su dakaci sabbin bayanai nan da sa'o'i 72.
Shugaban ya kuma yi nuni da cewa ƙungiƴar za ta iya janye yajin aikin da take yi, rahoton Daily Trust ya tabbatar.
A kalamansa:
"Zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a ranar Laraba, an dakatar da ita. Sannan za mu sake yin duba dangane da ita nan da sa'o'i 72."
Akpabio ya magantu bayan ganawa da likitoci
A cikin wata sanarwa da ofishin shugaban majalisar dattawa ya fitar, Akpabio ya yaba wa likitocin bisa dakatar da zanga-zangar da kuma ƙoƙarin janye yajin aikin da su ke yi.
Akpabio ya bayyana cewa ana sane da dukkanin buƙatun likitocin sannan za a biya musu su nan ba da daɗewa ba ana naɗa ministan lafiya.
Shugaban majalisar dattawan ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu ya damu da likitoci wanda hakan ne ya sanya ya naɗa likitoci masu yawa a cikin majalisar ministocinsa.
Tinubu Ya Amince a Ba Likitoci Alawus
A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinibu ya amince da biyan N25,000 kuɗin alawus ga likitoci da ma'aikatan lafiya na gwamnatin tarayya.
Shugaban ƙasar ya ɗauki wannan matakin ne bayan likitoci sun shiga yajin aiki bisa rashin daidaiton da suka samu da gwamnatin tarayya.
Asali: Legit.ng