Shugaba Tinubu Ya Sake Sanya Labule Da Farfesa Okonjo-Iweala
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da Darekta Janar ta ƙungiyar kasuwanci ta duniya a fadsr shugaban ƙasa, ranar Talata a birnin tarayya Abuja
- A wajen taron kuma akwai Ali Pate, tsohon ƙaramin ministan lafiya wanda cikin ƴa. kwanakin nan majalisar dattawa ta amince da shi a matsayin ministan Tinubu
- Okonjo-Iweala da Ali Pate sun riƙe muƙaman ministoci a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan wanda ya sha kashi a hannun Muhammadu Buhari a zaɓen 2015
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da Farfesa Ngozi Okonjo-Iweala, Darekta Janar ta ƙungiyar kasuwanci ta duniya (WTO), ranar Talata, 8 ga watan Agusta, a fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock Villa a birnin tarayya Abuja.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa tsohuwar ministan kuɗin ta iso fadar shugaban ƙasa ne da misalin ƙarfe 2:50 na rana.
Haka kuma a wajen taron akwai tsohon ministan lafiya, Dr Ali Pate, wanda kwanannan aka tantance da amincewa ya zama minista a gwamnatin Shugaba Tinubu.
Farfesa Okonjo-Iweala ta riƙe muƙamin ministan kuɗi da ministan kula da tattalin arziƙi tare da Pate, a ƙarƙashin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ƙarshen watan Yunin 2023, Shugaba Tinubu ya gana da Farfesa Okonjo-Iweala a karon farko tun bayan rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa, a wajen wani taro a ƙasar Faransa.
Ganawar ta su ta yau na zuwa ne bayan Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da kwamitin kawo gyare-gyare kan karɓar haraji a ƙasar nan, wanda Taiwo Oyodele zai jagoranta.
Menene dalilin ziyarar Okonjo-Iweala?
Da take tattaunawa da manema labarai bayan gana wa da Shugaba Tinubu, Okonjo-Iweala ta bayyana cewa ita da Pate sun tattauna da shugaban ƙasar ne kan yadda za su taimaki ƙasar nan "a yanayin da ake ciki yanzu".
Yanzu-Yanzu: ECOWAS Ta Sake Sanya Sabbin Takunkunmi Kan Juyin Mulkin Jamhuriyar Nijar, Bayanai Sun Fito
Ta bayyana cewa duk da ziyarar aiki ta kawo ba, akwai buƙatar ta bayar da dukkanin gudunmawar da za ta iya bayar wa a matsayinta na ƴar Najeriya, rahoton Daily Trust ya tabbatar.
Okonjo-Iweala tace ita da Pate a shirye su ke domin bayar da gudunmawa ga al'ummar Najeriya.
Tinubu Ya Nada 'Yar Jami'a Cikin Kwamiti
A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da kwamitin yin gatambawul kan haraji a ƙasar nan.
A cikin ƴan kwamitin wanda Taiwo Oyodele zai jagoranta har da Orire Agbaje, ɗalibar ajin ƙarshe a jami'ar Ibadan.
Asali: Legit.ng