Tinubu Ya Fada Mana A Gida Mai Dakuna 2 Ya Ke Zaune, Shugaban NLC Ya Yi Bayani

Tinubu Ya Fada Mana A Gida Mai Dakuna 2 Ya Ke Zaune, Shugaban NLC Ya Yi Bayani

  • Shugaban Kungiyar NLC, Joe Ajaero ya bayyana abin da Shugaba Bola Tinubu ya fada musu yayin da su ke ganawa da shi
  • Ajaero ya ce shugaban ya fada musu cewa a gida mai dauke da dakuna biyu ya ke kwana don rage yawan kashe kudade na gwamnati
  • Ajaero ya bayyana haka ne a yau Talata 8 ga watan Agusta a Abuja yayin hira da gidan talabijin na Channels

FCT, Abuja – Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC), Joe Ajaero ya ce Shugaba Bola Tinubu ya fada wa kungiyar cewa ya na rayuwa a gida mai dakuna biyu saboda rage yawan kashe kudaden gwamnati.

Ajaero ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a yau Talata 8 ga watan Agusta a Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Amsa Kira, Ya Bai Wa Dan Ibo Babban Mukami a Gwamnatinsa

Kungiyar NLC ta bayyana abin da Tinubu ya fada musu don rage yawan kashe kudade
Kungiyar NLC Ta Bayyana Abin Da Shugaba Tinubu Ya Fada Mata Don Rage Kashe Kudade A Gwamnati. Hoto: DOlusegun (Twitter).
Asali: Twitter

Kungiyar Kwadago ta janye zanga-zangar da take yi a ranar Alhamis 3 ga watan Agusta bayan ganawa da shugaban kasa, Bola Tinubu.

Tinubu ya yi korafi kan yawan kashe kudaden gwamnati

Yayin hirar, Ajaero ya ce Tinubu ya fada musu irin yadda ya ke jin bakin ciki ganin yadda gwamnati ke kashe kudade.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

“Lokacin da muke ganawa da Shugaba Tinubu ya yi korafi kan yawan kashe kudade na gwamnati.
“Mun fada masa cewa idan ya nada ministoci, su ma za su nada masu ba su shawara, sannan su ma za su nada masu taimaka musu.
“Amma Tinubu ya ce mu kawar da kai a kan haka, mu dubi hakan ta fuskar samar da aikin yi, amma ba mu amince da shi ba.”

Tinubu ya fadawa NLC yadda ya ke kwana a gida mai dakuna biyu

Kara karanta wannan

Ku Yi Hakuri: Shugabannin 'Yan Bindiga a Arewa Sun Nemi Afuwa, Za Su Ajiye Makamai

Ajaero ya kara da cewa kamar yadda Daily Trust ta tataro:

“Ya ba da misali da kansa, inda ya ce ya rage yawan motocinsa, an fada masa cewa haka na da alaka da matsalar tsaro.
“Ya kara da cewa, ya fi son ya yi amfani da jirginsa na musamman ba na gwamnati ba, amma muka ce masa a’a saboda tsaro ya kamata ya yi amfani da jirgin gwamnati, inda ya ce mana ya na kwana ne a gida mai dakuna biyu kacal.
“Ya ce ya na kokarin kara kaimi wurin tabbatar da cewa ya yi magana da wadanda su ke aiki tare, amma ban fahimci meye hakan ke nufi ba.”

FG Na Tattaunawa Da NLC Kan Tallafin Kudade Na Tinubu Bayan Cire Tallafi

A wani labarin, Gwamnatin Tarayya na ganawar gaggawa da kungiyar NLC don shawo kan matsalar zanga-zanga da kungiyar ke yi.

Kara karanta wannan

“Allah Ya Nuna Mani”: Shin Shugaban Kasa Tinubu Zai Kammala Wa’adinsa a Mulki? Malamin Addini Ya Yi Hasashe

Kungiyar na zaman ne da kwamitin ba da tallafi na shugaban kasa kan cire tallafin da aka yi a kasar.

Shugaban ma'aikata Femi Gbajabiamila shi ke jagorantar ganawar da sauran mambobin kwamitin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.