Dakarun Sojoji Sun Murkushe Yan Bindiga 10 a Wata Jihar Arewa, Sun Ceto Mutum 6
- Rundunar sojojin Najeriya ta yi gagarumin nasara a kan yan bindigar da suka addabi al'ummar jihar Zamfara
- Dakarun Operation Hadarin Daji sun murkushe yan bindiga 10 a wani samame da suka kai mabuyarsu a tsakanin Gadan Zaima da Dan Marke a karamar hukumar Bukkuyum
- Sun kuma yi nasarar ceto wasu mutane shida da yan bindigar suka yi garkuwa da su a wani jeji da ke tsakanin Mahuta da Zuru na jihar Kebbi
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Zamfara - Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadarin Daji (OPHD) a arewa maso yamma sun murkushe yan bindiga 10 arewa maso yammacin jihar Zamfara.
An tattaro cewa an kashe yan bindigar ne a wani kautan bauna da dakarun suka kai a hanyar da ke tsakanin Gadan Zaima da Dan Marke a karamar hukumar Bukkuyum, a ranar Talata, 8 ga watan Agustan 2023.
Majiyoyin sirri sun sanar da Zagazola Makama, kwararren masanin harkar tsaro a yankin tafkin Chadi cewa dakarun sun yi nasarar kashe yan bindiga da dama sannan suka ceto mutane shida da aka yi garkuwa da su a wani jeji da ke tsakanin Mahuta da Zuru na jihar Kebbi.
Ya ce bayan zazzafan musayar wuta da suka yi, dakarun sojin sun yi nasarar kama wasu yan bindiga da ransu sannan sun kwato bindigogin AK-47 shida, bindigar toka na GPMG, tsabar kudi sama da miliyan daya, wayoyin hannu da ganyen wiwi.
Kwamandan rundunar hadin gwiwar na OPHD, Manjo Janar Godwin Murkut, ya yaba ma kokarin dakarun sannan ya bukace su da kada su yi kasa a gwiwa har sai sun kakkabe gaba daya sansani da mabuyar yan bindigar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Har ila yau, dakarun sojojin atisayen 'Operation Hadin Kai' tare da haɗin gwiwar ƴan sakai (CJTF) sun halaka mayaƙan Boko Haram a dajin Sambisa.
A jihar Katsina kuwa, rundunar 'yan sandan jihar Katsina, ta sanar da ƙwato wasu mutane 5 daga hannun masu garkuwa da mutane da suka yi garkuwa da su.
Asali: Legit.ng