Hukumar ICPC Ta Waiwayo Kan Minista kuma Surukin Tsohon Shugaba Buhari
- Hukumar ICPC ta tabbatar da cewa jami’anta su na yin binciken da ya dace a game da Abubakar Malami SAN
- Tun tuni ‘Yan Human and Environmental Development Agenda su ke aikawa ICPC takarda, a binciki Lauyan
- ‘Dan siyasar ya shafe shekaru sama da bakwai daga 2015 a matsayin babban lauyan Gwamnatin tarayya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Hukumar ICPC mai binciken barayin gwamnati da sauran makamantan laifuffuka ta na bincike a kan tsohon Minista, Abubakar Malami.
Jaridar Punch ta ce hukumar ta na yin bincike ne game da zargin cin amanar ofishinsa da ya yi a lokacin da ya kasance Ministan shari’a na tarayya.
Tun daga karshen shekarar 2015 har zuwa watan Mayun 2023, Abubakar Malami SAN ne Ministan shari’a kuma babban lauya na gwamnatin tarayya.
H.S. Folaranmi ya fitar da wasika
An fahimci cewa ana binciken ne daga wata takarda da H.S. Folaranmi ya sa hannu a madadin shugaan hukumar ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An sa hannu a takardar ne a ranar Laraba, 19 ga watan Yuli 2023. H.S. Folaranmi shi ne babban jami’I mai karbar korafin jama’a a hukumar ICPC.
Hakan ya na zuwa ne bayan wata kungiya mai suna HEDA ta rika aikawa ICPC korafin cewa tsohon Ministan shari’an ya tafka rashin gaskiya.
Sahara Reporters ta ce baya ga haka, ana jifan Abubakar Malami da zargin saba doka. Zuwa yanzu ba a gudanar da bincike, an tabbatar da hakan ba.
"Ina rubuto maku wannan domin sanar da ku mun karbi korafinku a kan batun da yake sama, kuma ina sanar makuana daukar matakin da ya dace.
- H.S. Folaranmi
Saida jirgin ruwa
Wani zargin da ake yi masa shi ne yin gwanjon wani jirgin ruwa da ya dauko gwamnatin tarayya mai baya ga zargin biyan wasu lauyoyi daloli.
Tun a shekarar 2008, Malami ya samu karin girma zuwa babban lauya watau SAN ya na cikin wadanda su ka fi kowa dadewa a ofishin AGF a tarihi.
Surukin Shugaban Najeriya
Abubakar Malami ya na da kyakkyawar dangantaka da Muhammadu Buhari tun a jam’iyyar CPC, daga baya aka ji ya auri diyar shugaban kasar lokacin.
Amaryarsa, Hadiza Muhammadu Buhari ta taba auren Abdulrahman Mamman Kurfi wanda bincike ya bayyana cewa suna da 'ya'ya shida wannan mutum.
Asali: Legit.ng