Abba Gida Gida Ya Rantsar Da Mace Ta Farko Alkaliyar Alkalai A Jihar Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rantsar da mace ta farko a matsayin alkaliyar alkalan jihar
- Abba Kabir ya rantsar da Dije Audu Aboki a dakin taro da ke fadar gwamnatin jihar a yau Litinin 7 ga watan Agusta
- Dije ta godewa gwamnan da damar da ya ba ta inda ta yi alkawarin kawo sauyi a harkar shari'a da dawo da martabarta
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, ya kafa tarihi bayan rantsar da mace ta farko Dije Audu Aboki a matsayin alkaliyar alkalan jihar.
Abba Gida Gida ya rantsar da Dije ne a dakin taro na Africa House da ke fadar gwamnatin jihar a yau Litinin 7 ga watan Agusta.
Abba Kabir ya nemi goyon bayan Dije don rushe gine-gine ba bisa ka'aida ba
Abba Kabir ya roki bangaren shari'a da su marawa gwamnatinsa baya wurin rushe gine-gine ba bisa ka'ida ba, Aminiya ta tattaro.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya jaddada amfani da muhimmancin hadin kai tsakanin bangarorin gwamnati guda uku da suka hada shari'a da majalisu da zartarwa.
Ya ce:
"Dankantakar da ke tsakanin bangarori uku na gwamnati kamar su zartarwa da shari'a da kuma majalisa babu gaba."
Abba Kabir ya ce gwamnatinsa za ta inganta harkar shari'a
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta himmatu wurin inganta alaka tsakanin bangarori uku na gwamnatin, cewar gidan talabijin na Channels.
Abba Gida Gida ya yabi Dije Aboki kan jajircewarta da kuma kwarewa a harkar shari'a, cewar The Guardian.
Ya kara da cewa:
"Dije ta yi aiki a fannin shari'a wurin jajircewarta da kwarewa da kuma kishin kasa, inda yanzu Allah ya saka mata da babbar alkaliyar alkalai."
Abba Gida Gida Na Kano Na Bukatar Fiye Da Biliyan 6 Don Samar Da Kujerun Zama A Makarantun
A wani labarin, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinsu na bukatar Naira biliyan shida don samar da kujerun makarantun jihar.
Gwamnatin ta ce akalla makarantun firamare da sakandare fiye da 9,000 ne ke bukatar kujerun zama don inganta karatunsu.
Kwamishinan ilimi a jihar, Haruna Umar Doguwa shi ya bayyana haka a ranar Laraba 2 ga watan Agusta a Kano yayin karban bakwancin hukumar UNICEF.
Asali: Legit.ng