Mahaifina Ya Rasu Ne Sakamakon Sakacin Likita a Asibiti Mai Zaman Kansa, Sanata Umahi Ya Yi Bayani

Mahaifina Ya Rasu Ne Sakamakon Sakacin Likita a Asibiti Mai Zaman Kansa, Sanata Umahi Ya Yi Bayani

  • Sanata Dave Umahi ya bayyana yadda sakacin likitoci ya yi sanadin rasuwar mahaifinsa
  • Ya ce wani babban likita ne ya tura shi asibitinsa domin bai wa mahaifin na sa kulawa a can saɓanin asibitin gwamnati
  • Ya bayyana hakan ne a yayin da yake miƙa tambayoyinsa ga Mariya Mahmoud da aka tantance cikin ministocin Tinubu

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya bayyana yadda mahaifinsa ya rasu sakamakon sakacin da ma’aikatan lafiya suka yi a wani asibiti mai zaman kansa da bai bayyana sunansa ba.

Sanatan wanda ke wakiltar Ebonyi ta Kudu, ya bayyana hakan ne a lokacin da ake tantance Mariya Mahmoud, wacce aka ba da sunanta matsayin minista daga Kano kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Dave Umahi ya bayyana yadda likita ya janyo sanadin rasa ran mahaifinsa
Sanata Umahi ya bayyana yadda mahaifinsa ya rasu saboda sakacin likita. Hoto: Governor David Nweze Umahi
Asali: Facebook

Likitocin gwamnati na bude asibitoci masu zaman kansu

Kara karanta wannan

‘Yadda Cire Tallafin Man Fetur Ya Tunzura Ni Aikata Fashi Da Makami’, Direba Ya Yi Bayani

Umahi wanda shi ma yana cikin mutanen da aka ba da sunansu a cikin minstoci 48 da Tinubu zai naɗa, ya jefawa Dakta Mariya tambaya kan yadda za ta magance matsalar tarewar da likitocin gwamnati ke yi a asibitoci masu zaman kansu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bayyana cewa, lokacin da aka kai mahaifinsa asibitin gwamnati, sai likitan da ke kan aiki ya tura su zuwa wani asibiti mai zaman kansa wanda mallakinsa ne.

Ya ce sakacin da likitan ya yi a asibitin ne ya janyo rasuwar mahaifin na sa kamar yadda Channels TV ta wallafa.

Mariya ta ce za su magance matsalar da ake samu a bangaren likitoci

Da take mayar da martani kan tambayar, Mariya Mahmoud wacce ta kasance ma'aikaciyar asibiti ce, ta ce za su ɗauki mataki kan matsalar idan ta samu dama.

Kara karanta wannan

Kitimurmura: Soja mace ta fusata, ta harbe na gaba da ita a wurin aiki a jihar Arewa

Ta amince da cewar ana samun matsaloli a barin aikin da likitocin gwamnati ke yi su tafi asibitocinsu masu zaman kansu.

Mariya Mahmoud ita ce ta maye gurbin Maryam Shetty, wacce aka cire sunanta a daidai lokacin da ake shirin tantance ta.

Ganduje ya yi bayani kan dalilin cire sunan Maryam Shetty

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan dalilin cire sunan Maryam Shetty daga ministocin Tinubu da aka bayyana.

Tsohon gwamnan jihar Kano, kuma shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce 'yan ba ni na iya ne suka sanya sunanta tun da farko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng