Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Wani Da Ake Zargi Da Kashe Makwabcinsa, Ta Fadi Dalili
- Babbar kotu da ke zamanta a Ilorin da ke jihar Kwara ta yanke wa wani mutum hukunci bayan ya kashe wani ango makwabcinsa
- Wanda ake zargin mai suna Mohammed Kazeem ya kashe makwabcin nasa ne ana saura kwanaki kadan ya zama ango
- Kotun da ke zamanta a Ilorin babban birnin jihar ta yanke wannan hukunci ne a ranar Alhamis 3 ga watan Agusta
Jihar Kwara – Babbar kotun da ke zamanta a Ilorin da ke jihar Kwara ta yanke wa wani hukuncin kisa bisa zargin kashe makwabcinsa Olokose Ojo Olushola.
Wanda ake zargin mai suna Mohammed Kazeem Beiwa ya kashe makwabcin nasa ne ana saura kawanaki kadan ya zama ango.
Kotun ta yanke wannan hukuncin kisan ne a kan Kazeem a ranar Alhamis 3 ga watan Agusta a kotun da ke Ilorin, Aminiya ta tattaro.
Alkalin kotun ya yanke hukunci
Alkalin kotun, S. M Akanbi ya ce kotun ta samu mutane uku da ake zargi da hannu cikin kisa yayin da kotun ta wanke mutum na hudu saboda hujjojin da aka kawo, cewar Punch.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Akanbi ya kuma yanke hukunci daurin shekaru 10 da biyan tarar kudi har Naira dubu 100 ga mutane biyu da ake zargi da hannu cikin kisan da suka hada da Madu Jeremiah da Mohammed Chatta.
Lauyoyin masu shigar da kara sun bayyana yadda kisan ya faru
Lauyan masu shigar da kara kuma kwamishinan shari’a, Ibrahim Sulyman ya ce wanda ake zargi ya sace marigayin ya boye shi kafin daga baya ya kashe shi a gidansa, Daily Post ta tattaro.
Ya kuma kara da cewa Kazeem bayan kashe marigayin ya yi gunduwa-gunduwa da gawarsa sannan ya nemi kudin fansa bayan kashe shin da ya yi.
Lauyoyin masu shigar da kara sun gabatar da shaidu tara a gaban kotun tare da hujjoji masu yawa da za su iya gaskata abin da su ke zargi.
"Ban San Yadda Aka Yi Na Samu Ciki Ba Tare Da Kwanciyar Aure": Matar Aure Ta Fada Wa Kotu
A wani labarin, wata mata ta fada wa kotu cewa ba ta san yadda aka yi ta samu ciki ba, ba tare da kwanciyar aure ba.
Matar mai suna Taibat Abubakar ta na neman saki ne daga kotun inda ta ce ba za ta iya bayanin yadda ta samu ciki ba.
Asali: Legit.ng