'Yan Sanda Sun Yi Nasarar Kuɓutar Da Mutane 5 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane a Katsina

'Yan Sanda Sun Yi Nasarar Kuɓutar Da Mutane 5 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane a Katsina

  • Rundunar 'yan sandan jihar Katsina, ta sanar da kuɓutar da mutane 5 daga hannun masu garkuwa da mutane
  • Jami'an 'yan sandan sun yi nasarar kuɓutar da mata uku, yaro ɗaya da magidanci da aka ɗauke daga ƙaramar hukumar Malumfashi
  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Katsina, ASP Abubakar Sadiq ne ya bayyana hakan a ranar Litinin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Katsina - Rundunar 'yan sandan jihar Katsina, ta sanar da ƙwato wasu mutane 5 daga hannun masu garkuwa da mutane da suka yi garkuwa da su.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq ne ya bayyana hakan ga manema labarai, ranar Litinin a birnin Katsina.

Yan sandan jihar Katsina sun yi musayar wuta da 'yan ta'adda
'Yan sandan jihar Katsina sun yi nasarar kuɓutar da mutane 5 daga hannun masu garkuwa. Hoto: Katsina Post
Asali: Facebook

Matan aure 3 yaro 1 da magidanci guda 1 ne suka ɗauke

Sadiq ya ce lamarin ya faru ne a ƙauyen Sabon Gida, da ke ƙaramar hukumar Malumfashi da ke jihar ta Katsina, inda masu garkuwar suka yi awon gaba da mata uku, yaro 1 da magidanci guda ɗaya.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Hallaka Manomi, Sun Sace Mata 5 Da Maza 2 a Kaduna

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce jami'ansu da ke ƙaramar hukumar Kankara, sun samu rahoton cewa wasu mutane ɗauke da bindigu ƙirar Ak 47, sun kai hari gami da ɗauko mutane biyar daga ƙauyen kuma sun nufo Kankara da su.

Ya ce jim kaɗan bayan samun rahoton ne DPO na Kankara ya jagoranci mutanensa zuwa wurin, inda suka yi musayar wuta wacce ta yi sanadiyar arcewar 'yan ta'addan ba tare da ko mutum ɗaya ba.

Ya ƙara da cewa yanzu haka jami'an na su na ƙoƙarin bin sawun masu garkuwar domin kamo su don fuskantar tuhuma kamar yadda aka wallafa a shafin Channels TV.

'Yan sanda sun kama masu aikata miyagun laifuka 30 a Katsina

A wani rahoto da jaridar Vanguard ta wallafa a kwanakin baya, rundunar 'yan sanda jihar Katsina ta sanar da kamar mutane 30 da ake zargi da aikata laifuka a jihar.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Farmaki Gidan Gonan Sanata a Arewa, An Rasa Rai

Haka nan a yayin kamen, 'yan sandan sun yi nasarar ƙwato shanun da aka sace gami da kuɓutar da mutane da dama da aka ɗauke.

Haka nan a wani labari da Legit.ng ta wallafa a baya, kun karanta labarin 'yan ta'adda 22 da sojojin sama suka halaka a Batsari da ke jihar ta Katsina.

Legit.ng har ila yau ta kuma kawo muku rahoton wani babban basarake da masu garkuwa da mutane suka sace a jihar Nassarawa tare da mai ɗakinsa a ranar Lahadin da ta gabata.

An gargaɗi 'yan Najeriya kan tafiye-tafiye zuwa Nijar

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan gargaɗin da hukumar kula da shige da fice ta Najeriya ta yi wa 'yan ƙasa dangane da tafiye-tafiye zuwa Nijar.

Kwanturolan hukumar da ke kula da iyakar Najeriya da Nijar da ke Jibia ta jihar Katsina, Mustapha Sani ne ya yi wannan gargadi.

Kara karanta wannan

Hadi Sirika Ya Bayyana Halin Da Mutanen Da Suka Yi Hadari a Jirgi Mai Saukar Ungulu a Legas Ke Ciki

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng