Taoreed Lagbaja Ya Ce Sojoji Za Su Ci Gaba Da Kare Dimokuradiyyar Najeriya

Taoreed Lagbaja Ya Ce Sojoji Za Su Ci Gaba Da Kare Dimokuradiyyar Najeriya

  • Babban hafsan sojojin Najeriya, Taoreed Lagbaja, ya yi magana gameda dimokuraɗiyyar Najeriya
  • Ya ce sojojin Najeriya ba za su ba da goyon baya wajen raunata dimokuraɗiyya ba balle kuma kawar da ita
  • Ya yi wannan iƙirarin ne a daidai lokacin da ake fargabar yiwuwar samun yaƙi tsakanin ECOWAS da sojojin Nijar

Jaji, Kaduna - Babban hafsan sojojin Najeriya Taoreed Lagbaja, ya ce a ko da yaushe sojojin Najeriya za su kare tare da ƙarfafa dimokuraɗiyyar ƙasar nan.

Lagbaja ya yi wannan jawabi ne a ranar Asabar, a wajen bikin yaye ɗaliban makarantar sojojin Najeriya da ke garin Jaji na jihar Kaduna kamar yadda aka wallafa a shafin rundunar sojin na Twitter.

Lagbaja ya yi magana kan dimokuraɗiyyar Najeriya
Babban hafsan sojojin Najeriya ya ce za su ci gaba da kare dimokuraɗiyyar Najeriya. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Ya buƙaci sojoji su guji sanya siyasa cikin ayyukansu

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Dalilin Da Ya Sanya Yakamata Najeriya Ta Sake Dawo Da Doka Da Oda a Nijar, Reno Omokri Ya Bayyana

Lagbaja ya yi kira ga sojojin da aka yaye da su zama gwarazan da dimokuraɗiyyar za ta yi alfahari da su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya bayyana cewa abinda kawai ya fi dimokuraɗiyya a wannan zamani da muke ciki, shi ne ci gaba da tabbatuwar tsarin dimokuraɗiyya.

Ya kuma buƙaci sojojin da su guji sanya siyasa wajen gudanar da ayyukansu daidai da yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada kamar yadda The Cable ta wallafa.

Lagbaja ya kuma ba da tabbacin cewa sojojin ba za su taɓa ba da gudunmawa wajen raunata dimokuraɗiyya ba, ballantana kuma kawar da ita.

Alaƙar jawaban na Lagbaja da juyin mulkin Nijar

Wannan jawabi na Lagbaja na zuwa ne dai a cikin ƙasa da makonni biyu da sojojin jamhuriyar Nijar suka kifar da gwamnatin dimokuraɗiyya mai ci a ƙasar.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Hambararren Shugaban Nijar Bazoum Ya Aike da Sabon Saƙo Ga Amurka da Wasu Ƙasashe

Sojojin Nijar ƙarƙashin jagorancin dakarun da ke tsaron fadar shugaban ƙasa, Abdourahmane Tchiani ne suka wuntsilar da gwamnatin Muhammed Bazoum a ranar Laraba, 26 ga watan Yulin da ya gabata.

Hakan ya janyo kakkausar suka daga sassa daban-daban na duniya, ciki kuwa har daga ƙungiyar ECOWAS da ta bai wa sojojin wa'adin kwanaki 7 don su mayar da mulkin ga farar hula.

Shugaban juyin mulkin jamhuriyar Nijar ya yi sabbin naɗe-naɗe

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan sabbin naɗe-naɗen da shugabannin juyin mulki na jamhuriyar Nijar suka yi.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da wa'adin da ƙungiyar ECOWAS ta bai wa sojojin na su mayar da mulki zuwa ga farar hula ke kammala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng