Yadda Wani Mutum Ya Fasa Taro a Wurin Biki, Ya Dura da Jaka ‘Ghana-Must-Go’ Cike Da ’Yan N10 da N5

Yadda Wani Mutum Ya Fasa Taro a Wurin Biki, Ya Dura da Jaka ‘Ghana-Must-Go’ Cike Da ’Yan N10 da N5

  • Wani dan Najeriya ya halarci bikin daurin aure da wata Jakar ‘Ghana Must Go’ cike da kudi ‘yan N10 da N5 kawai
  • Mutumin mai suna Chulo Ways, wasu mutane biyu ne da suka yi kama-kama wajen dauko masa tarin kudaden kamar wani attajiri
  • Chulo ya yi amfani da kudin ne wajen lika wa ma'auratan, amma wasu da suka kalli bidiyon a TikTok sun ce kudin bai ma kai N50k ba duka

Wani dan Najeriya ya dura wurin bikin daurin aure dauke da Jakar ‘Ghana Must Go’ cike da kudi ‘yan N10 da N5.

Mutumin mai suna Chulo Ways ya dura wurin liyafar daurin auren ne tare da wasu jami’an tsaro guda biyu wadanda suka taimaka masa wajen daukar jakar kudin.

Chulo Ways, wanda kuma aka fi sani da Odogwu Ten Five, an san shi da fankama da kananan kudaden Naira.

Kara karanta wannan

Ku Yi Hakuri: Shugabannin 'Yan Bindiga a Arewa Sun Nemi Afuwa, Za Su Ajiye Makamai

Yadda wani ya dura wurin daurin aure da 'yan N5 da N10
Lokacin da ya dura wurin daurin auren | Hoto: @chulo_wayz.
Asali: TikTok

Lokacin da ya shiga wurin daurin auren, tuni ya zuge jakar, sai ya fara diba yana lika wa amarya da ango a lokacin da suke tika rawa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda aka kaya a wurin bikin

MC din da ke kara tunzura lamarin bikin ya yabawa Chulo Ways yayin da yake ci gaba da cire takardun kudi na ‘yan N10 da N5 yana manni.

Wasu masu amfani da TikTok sun yi ta cece-kuce tare da cewa gaba dayan kudin ma da ke cikin jakar ba su wuce N50k ba.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a bayan ganin bidiyon

@pluto ya ce:

"Ba kowa ne da hankali ba fa a kasar nan."

@Damsel Lizzy yayi sharhi:

"Kila tsohon saurayin amaryar be."

@khriztoph ya ce:

"Duk kudin ba su kai 50k ba."

@Mimi tace

"Kenan ma babu wanda ya lura cewa kudin ya yi amfani da shi wajen dinka kayan da yake jikinsa.

Kara karanta wannan

Kitimurmura: Soja mace ta fusata, ta harbe na gaba da ita a wurin aiki a jihar Arewa

@ mai amfani5622954952856 ya ce:

"Na tabbata tsohon saurayinta ne."

@oluomachindubuisi said:

"Ni kadai da iyalai na ne masu hankali a kasar nan."

@Linfroshgold ya ce:

"Matar ta bude baki tana kallo kamar mai cewa waye wannan mutumin."

@Ella ta ce:

"Dukkan kudin ba su kai N20k ba."

@I'amWinner ya ce:

"Wannan ai ciwon kai ne ga duk wanda aka ba ya kirga kudin."

@etuwejuliet@chi said:

"Amarya ta tunzura fa."

Yadda wani bikin kuma ya tarwatse

A wani labarin, an tarwatse daga wajen wani taron biki bayan an gano cewa angon yana da aure har da 'ya'ya bakwai.

Wani shaidar gani da ido wanda ya kawo rahoton a TikTok ya nuna wurin taron bikin, wanda mutane suka watse daga wajen.

Wasu mutane na makale a wurare daban-daban yayin da akayi fata-fata da kayan kwalliyar da aka yiwa wurin taron bikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.