Gwamnatin Najeriya zata rage farashin abinci
Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wani kwamiti da zai duba yadda za a inganta hanyoyin samar da abinci a kasar da kuma saukar da farashinsa a kasuwanni.
Makaddashin shugaban kasar Yemi Osinbajo ya ce an dauki matakin ne domin magance matsalar tsadar kayan abinci da kasar ke fama da ita a baya-bayan nan.
Farashin kayayyaki sun yi tashin gwauron zabi, abin da ya kara jefa 'yan kasar cikin mummunan hali.
KU KARANTA KUMA: Sojoji sun kwato makamai, motoci bayan arangama da yan Boko Haram
Najeriya na fuskantar matsalar tattalin arziki mafi muni cikin shekara 20 sakamakon faduwar darajar danyan mai a kasuwannin duniya.
A lokacin da ya ke bayar da umarni a wata ganawa da ya yi da majalisar zartarwa, Mista Osinbajo ya nuna damuwarsa a kan hauhawar wasu kayayyakin abinci.
Ya ce kwamitin da aka kaddamar zai ta duba hanyoyin da za a bi domin inganta samar da abinci a farashi mai sauki ga 'yan Najeriya.
Duk da rahotannin da ke cewa amfanin gonaki sun yi yabanya a sassa daban-daban na kasar, farashin abinci na kara hawa.
Wasu kayan amfanin gonar kuma na lalacewa sakamakon rashin ingantacciyar hanyar da za a bi domin sufurin kayan zuwa kasuwanni ko kuma adana su.
A cewarsa, kwamitin wadda aka bai wa wa'adin kwana bakwai daga ranar Laraba domin gabatar da rahotonta, zai duba yiwuwar kawar da abubuwan da ke haddasa hauhawar farashi a tsakanin gonaki da kasuwanni.
KU KARANTA KUMA: Osinbajo ya jagoranci taron majalisa a bayan Buhari
Mista Osinbajo ya ce yin haka zai kawo sauki ga al'ummar kasar.
Farashin wasu abubuwa a watan Janairun 2016 zuwa Janairun 2017
1. Buhun shinkafa babba N8000 - N19,500
2. Buhun Semovita N1,300 - N3000
3. Buhun fulawa N6,000 - N12,000
4. Kwanon dawa - N140 - N600
5. Kwanon wake N400 - N800
6. Kwanon sikari N400 - N900
7. Indomie N35 - N70
8. Tulun gas matsakaici (kilo 12.5) N2,500 - N5,300
9. Litar kananzir N100 - N500
Kwamitin na karkashin ministoci kamar haka: Ministan Gona Chief Audu Ogbeh, Ministan Kudi Misis Kemi Adeosun, Ministan Kasuwanci Okey Enelamah, Ministan Sufuri Rotimi Amaechi, Ministan Ruwa Suleiman Adamu da kuma Ministan Kwadago Chris Ngige
Asali: Legit.ng