Shugabannin ’Yan Bindiga Sun Roki a Tausaya Musu, Gwamnati Ta Yi Hakuri Ta Yafe Musu, Za Su Aje Makamai

Shugabannin ’Yan Bindiga Sun Roki a Tausaya Musu, Gwamnati Ta Yi Hakuri Ta Yafe Musu, Za Su Aje Makamai

  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, shugabannin ‘yan bindiga suna neman a yi musu afuwa a kasar nan
  • Sun bayyana hakan ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ragargazarsu da kuma kai hari maboyarsu a dazuka
  • Ya zuwa yanzu, sun tura sakon abin da suke bukata daga gwamnati da kuma kungiyoyin Fulani a fadin kasar nan

Jihar Zamfara - Wasu kasurguman ‘yan bindiga a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya musamman jihohin Katsina da Zamfara sun yi kira ga gwamnati da ta yi musu afuwa.

Leadership ta tattaro cewa hakan na faruwa ne saboda ci gaba da kai hare-haren bam da sojin Najeriya ke yi a maboyar tsageru a kasar.

A baya, an ruwaito yadda sojojin Najeriya suka hallaka ‘yan ta’addan, iyalansu da kuma tarin dabbobin da ake kyautata zaton sun sata ne.

Kara karanta wannan

Kitimurmura: Soja mace ta fusata, ta harbe na gaba da ita a wurin aiki a jihar Arewa

'Yan ta'adda na neman gafarar gwamnati
Jihar Zamfara, inda 'yan ta'adda ke aikin ta'addanci | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Tsageru sun yi nadamar shiga ta’addanci

An kuma tattaro cewa, ‘yan bindigan da aka ce sun yi nadamar shiga ta’addanci da sukayi, sun kuma tura tawaga zuwa wani taro da aka gudanar a kauyen Gusami da ke karamar hukumar Birnin Magaji a Zamfara inda suka bayyana bukatarsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda majiyar leken asiri ta PR Nigeria ta ruwaito, wasu daga cikin manyan tsagerun da wakilansu da sun hada da Usman Ruga Kachallah, Alaji Shingi, Lauwali Dumbulu, Shehu Bagiwaye, Sehu Karmuwal da Jarmi Danda.

A cewar majiyar, tabbas an ga wadannan da ke sama a wurin taron, inda suka bayyana neman afuwarsu ga gwamnatin kasar nan.

Ba za su ajiye dukkan makamai ba

A wurin taron, sun yi tayin kowa ya rungumi zaman lafiya tare da mika makamansu ga gwamnati idan aka karbi tubansu.

Kara karanta wannan

Maryam Shetty: ‘Yan Siyasa, ‘Yan Takara Da Mutane 5 Da Suka Ga Samu Da Rashi

Sai dai sun bayyana rokon kada su mika dukkan makamansu domin su kare kansu daga ‘yan ta’addan da basu ajiye makamai a yankunan Najeriya da Nijar.

Sun kuma bukaci jami’an kungiyoyin Fulani kamar kungiyar Miyetti da su shiga tsakani wajen samar da zaman lafiya da kawo shirin yafe musu laifukansu.

An kashe shugabannin ‘yan bindiga biyu a kasar nan

A wani labarin, rundunar sojin sama ta hallaka wasu jiga-jigan 'yan bindiga yayin luguden wuta daga sama a jihar Zamfara.

Yayin luguden wutan, rundunar ta yi nasarar hallaka wasu 'yan bindigan 10 da suka addabi yankunan Arewa maso Yamma.

Daily Trust ta bayyana sunayen 'yan bindigan da aka hallaka da Ado Aliero da Dankarami.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.