Tashin Hankali Yayin da Wata Jami’ar Soja Ta Sheke Oganta a Shingen Binciken Ababen Hawa

Tashin Hankali Yayin da Wata Jami’ar Soja Ta Sheke Oganta a Shingen Binciken Ababen Hawa

  • Yanzu muke samun labarin yadda wata mata soja ta hallaka babban jami’in da ya fi ta saboda hargitsi a jihar Adamawa
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da aka sanya dokar hana fita a jihar Adamawa da kuma yadda ake bukatar tabbatar da bin dokar
  • Ya zuwa yanzu, an kama sojar kuma an tabbatar da mutuwar jami’in da aka ce kyaftin ne a rundunar sojin Najeriya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Adamawa - Wata soja da ke aikin tabbatar da bin dokar hana fita da gwamnatin Adamawa ta sanya ta kashe wani babban jami’in soja a wani shingen bincike a Yola, babban birnin jihar.

Idan baku manta ba, Gwamna Ahmadu Fintiri ya sanya dokar ta-baci bayan da wasu ‘yan baranda suka kutsa rumbun gwamnati tare da wawashe kayayyakin abinci a jihar.

Kara karanta wannan

Takunkumi: Wata kasa za ta fara hana amfani da intanet cikin dare, ta fadi dalili

Majiyoyi sun shaida wa Daily Trust cewa matar sojar mai suna Nkiru ta bindige wani kaftin din soja ne da ya yi kokarin shiga tsakani a rikicin da ta ke da da jama’a a sha-tale-talen jihar.

Yadda wata soja ta hallaka mai gidanta a wurin aiki a Adamawa
Jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabashin Najeriya | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru

Majiyoyin tsaro sun shaida cewa, matar ta dage cewa dole ne masu ababen hawa da ke dawowa gida a lokacin dokar hana fita su koma inda suka fito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu daga cikinsu sun bayyana kansu a matsayin ma'aikata a fanni mai muhimmnaci amma ta tsaya tsayin daka dole sai sun bi maganarta, kamar yadda wani jami’in tsaro ya bayyana.

An ce an garzaya da wanda ta bindigen zuwa cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Yola, inda aka tabbatar da mutuwarsa, yayin da nan take sojoji suka kama matar da ta yi aika-aikan.

Kara karanta wannan

Innalillahi: An Tsinci Gawar Hadimin Fitaccen Sanata Da Raunin Harsashi

Halinta ne cin zarafin jama’a

An samu labarin cewa, an zargi matar soja da laifin cin zarafin jama’a, inda ta ke kokarin harba bindiga kan abin da bai kai ya kawo ba.

A lokacin da wakilin Daily Trust ya ziyarci hedikwatar Birgediya 23 da ke Yola domin tabbatar da hakan, Kwamandan wurin, Birgediya Janar Muhammad Gambo, ya aike da sakon cewa dole ne ‘yan jarida su nemi izinin a rubuce kafin ya yi magana da su.

Jigon APC ya gargadi sojojin Mali, Nijar da suke barazanar taran na Najeriya

A wani labarin, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya yi wani kakkausan gargadi ga shugabannin mulkin soja a Nijar, Mali da Burkina Faso kan abin da ya bayyana a matsayin barazana ga Najeriya.

Jigon na jam’iyyar APC mai mulki ya bukaci shugabannin da suka yi juyin mulki da kada su tunzura Najeriya a yanayi irin wannan.

Kara karanta wannan

Karen Mota Ya Yi Karambani da Tirelar Dangote, Ya Ɓurma Gida Ya Murƙushe Yara

Bayan juyin mulkin da aka yi a jamhuriyar Nijar a baya-bayan nan da ya hambarar da shugaban kasar Mohamed Bazoum, ECOWAS, ta ba gwamnatin mulkin soji a Nijar wa'adin kwanaki bakwai da ta dawo da hambararren shugaban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.