Marmari daga nesa: Jerin yadda girma da mukamai suke a gidan soja
Soja hausawa suka ce wai marmari daga nesa. Ko ma dai me kenan, sojoji wasu mutane ne masu matukar muhimmanci da kwarjini a cikin al'umma musamman ma idan aka yi la'akari da anfanin su wajen tsare kasa da mutanen cikin ta daga dukkan hadari.
Sai dai a lokuta da dama za ka samu mutane na cikin duhu game da yadda ainahin rabe-raben mukaman sojoji suke a kasa da ma kuma cewa ko waye babban wani a tsakanin su.
KU KARANTA: Wata mata ta haifi jariri mai fuska 2
Kamar dai dukkan wanni aikin gwamnati, suma sojoji suna da mukaman su kuma akan kara masu girma ne daga lokaci zuwa lokaci ko kuma idan bukatar hakan ta taso saboda jarumta ko kwazo.
Legit.ng dai ta tattaro mana yadda jerin mukaman na su suke kamar haka:
1. Field Marshal
2. Janar (General)
3. Laftanal Janar (Lieutenant General)
4. Manjo Janar (Major General)
5. Birgediya Janar (Brigadier General)
6. Kanal (Colonel)
7. Laftanal Kanar (Lieutenant Colonel)
8. Manjo (Major)
9. Keftin (Captain)
10. Laftanal (Lieutenant)
11. Laftanal na Biyu (Second Lieutenant)
12. Warant Ofisa I (Warrant Officer Class I)
13. Waran Ofisa II (Warrant Officer Class II)
14. Babban Sajant (Staff Sergeant)
15. Sajant (Sergeant)
16. Kofur (Corporal)
17. Karamin Kofur (Lance-corporal)
18. Firabet (Private)
19. Kurtu (Recruit)
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng