‘A Gaba Na Wani Ya Soye’: Bella Shmurda Ya Ba da Labarin Dalilin da Ya Sa Ya Daina Aiki a Kamfanin Dangote

‘A Gaba Na Wani Ya Soye’: Bella Shmurda Ya Ba da Labarin Dalilin da Ya Sa Ya Daina Aiki a Kamfanin Dangote

  • Shahararren mawakin Najeriya, Bella Shmurda kwanan nan ya bayyana daya daga cikin abubuwan da suka canza rayuwarsa zuwa yadda yake a yanzu
  • Bella, a wata hira da aka yi da shi a gidan radiyo a baya-bayan nan, ya ba da labarin wani mummunan hatsari da ya gani a lokacin da ya ke aiki masana’anta taliyar Dangote
  • Mawakin ya ce bayan ya ga daya daga cikin abokan aikinsa ya fada cikin tafasasshen mai ya soye ya mutu; nan ne ya rantse ya daina aikin kamfani, musamman na Dangote

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Najeriya - Shahararren mawakin Najeriya, Bella Shmurda ya haifar da cece-kuce a yanar gizo tare da bayyana wani mummunan abin da ya gani wanda ya sa ya daina aiki a kamfanin Dangote.

Mawakin ya bayyana cewa tun yana matashinsa, yana aji biyu a jami’ar jihar Legas, ya fara aiki saboda ya samu kudin kashewa, don haka ya yanke shawarar yin aiki masana’antar taliyar Dangote.

Kara karanta wannan

Innalillahi: An Tsinci Gawar Hadimin Fitaccen Sanata Da Raunin Harsashi

Bella ya ce ya dade yana aiki a masana'antar har sai da wata rana; ya ga yadda abokin aikinsa ya mutu bayan da ya kuskure ya fada cikin wani kwanon mai ya soye ya mutu.

Dangote: Mawaki ya bar aiki a kamfanin Dangote saboda wani ya soye a gabansa
Labarin da mawaki ya bayar na aiki a kamfanin Dangote | Hoto: @bellashmurda/@aliko_dangotegcon
Asali: Instagram

Mawakin ya lura cewa wannan abin da ya faru ya shafi lafiyar tunaninsa sosai, wanda ya sa ya yi murabus nan da nan bai dawo ba bakin aiki ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Martanin jama’a a kafar sada zumunta

Bayan ba da labarin, jama’ar kafar sada zumunta sun bayyana martaninsu kan abin da ya faru, inda suka bayyana ra’ayoyinsu. Ga kadan daga ciki:

@magamudi:

"Kuma ka sani, babu wanda aka biya diyya. Masu arziki a Najeriya suna gina arziki ne da jinin talakawa."

@raphaelokache:

"Na ji babu dadi ga marigayin amma har yanzu dai dariya nake."

Kara karanta wannan

Kitimurmura: Ministan Tinubu ya roki gafarar Sanatoci bayan kiransu wawaye a 2021

@tunnadex_moore:

"Wannan abin bakin ciki ne amma bayanin Bella ya sa abin ya bani dariya amma dai Dangote yin taliya ne Bella?"

@crisoke:

"Nima haka zan yi idan nine.”

@nature84:

"Ayya fatan an biya dangin yaron diyya."

@ehi15____:

"Labari mai ban tausayi amma yadda ya ba da shi ya ban dariya."

@sidney_leo:

"A gaskiya wannan labari ne mai ban tausayi, amma yadda Bella ya ambaci zafin, ya ba ni dariya."

Jarin Dangote ya karye da $400m, ya sauka a matsayinsa na mai kudin Afrika

A wani lavarin, Aliko Dangote dai ya sake samun koma baya a yawan kudinsa sakamakon faduwar darajar Naira, lamarin da ya rage darajar kadarorinsa da dukiyarsa na koma kasa da dala biliyan 11.

Arzikin attajirin na Najeriya ya ragu daga dala biliyan 11.2 a ranar 4 ga watan Agusta zuwa dala biliyan 10.8, ya samu faduwar dala miliyan 400 kenan a rana daya kacal a cewar Forbes.

Kara karanta wannan

‘Saura Kiris In Bakunci Lahira Saboda Kwankwadar Barasa’, In Ji Gogaggen Jarumin Fina-Finan Najeriya

A halin yanzu, a cikin jerin attajirai da aka sabunta a ranar 5 ga Agusta, 2023, Dangote ya koma matsayinsa na daya, inda dukiyarsa ta haura dala biliyan 13.5 ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.