Kasar China Ta Kawo Dokar Hana Amfani da Intanet a Cikin Dare, Ta Bayyana Dalilinta
- Kasar China ta sanya sabbin dokokin da za su hana yaraa kanana da matasa hawa shafukan sada zumunta a fadin kasar
- Wannan dokar za ta yi aiki ne da daddare domin matasan su yi amfani da lokutansu wajen yin abubuwa masu amfani
- Ba wannan ne karon farko da ake sanya dokoki masu tsauri ba a kasar, an sha yin hakan a lokuta mabambanta
Kasar China - Za a fara gimtse yara da matasa daga shiga shafukan intanet da daddare a kasar China, kuma za a hana su amfani da wayoyinsu a karkashin sabbin dokokin da aka kaddamar a ranar Laraba da nufin yakar maitar hawa intanet, NDTV ta ruwaito.
Karkashin dokar, wadda za ta fara aiki a ranar 2 ga watan Satumba bayan wata tattaunawa da jama'ar kasar suka yi, za a katse duk wanda bai kai shekaru 18 ba daga shiga shafukan intanet tsakanin karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.
Hakanan za'a sanya wani tsari na sarrafa lokacin amfani da wayoyin hannu, wanda zai ba da akalla mintuna 40 a rana ga wadanda basu kai shekaru takwas ba da kuma awa biyu ga wadanda suke shekaru 16 da 17.
Dokokin China kan yi tsauri idan aka kwatanta da na duniya
Sabbin dokokin da Hukumar Kula da yanar gizon kasar China (CAC) ta gabatar su ne mafi tsauri a yanzu a duniya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sai dai, rahotanni sun bayyana cewa, iyaye za su iya ketare wadannan dokokin da aka kawo idan sun so, kamar yadda Hong Kong Free Press ta ruwaito
CAC ta ce dokokin za su inganta tsarin amfani da kafafen yanar gizo tare da kirkirar hanyoyin ci gaba da kuma amfani da lokaci don yin abubuwa masu amfani ga masu tasowa.
Kasar China dai na daga cikin kasashen da ke yawan kawo dokokin da babu su a wasu kasashen duniya don inganta rayuwar ‘yan kasar.
China za ta yafewa kasashen Afrika bashi
A wani labarin, kasar China za ta cire wasu kasashen nahiyar Afrika daga cikin jerin kasashen da za su biya bashi marar kudin ruwa da ake saka ran kasashen zasu biya a karshen shekarar 2020.
Shugaban kasar China, Xi Jinping, ne ya bayyana hakan a cikin jawabin da ya gabatar yayin taron kara dankon zumunci tsakanin kasar China da kasashen nahiyar Afrika wanda aka yi ranar Laraba.
Yayin taron, wanda aka gudanar ta hanyar amfani da fasahar yanar gizo, Jinping ya ce za a karawa wasu kasashen nahiyar Afrika tsawon wa'adin biyan bashin da China ke binsu.
Asali: Legit.ng