China za ta yafewa kasashen Afrika bashi

China za ta yafewa kasashen Afrika bashi

Kasar China za ta cire wasu kasashen nahiyar Afrika daga cikin jerin kasashen da za su biya bashi marar kudin ruwa da ake saka ran kasashen zasu biya a karshen shekarar 2020.

Shugaban kasar China, Xi Jinping, ne ya bayyana hakan a cikin jawabin da ya gabatar yayin taron kara dankon zumunci tsakanin kasar China da kasashen nahiyar Afrika wanda aka yi ranar Laraba.

Yayin taron, wanda aka gudanar ta hanyar amfani da fasahar yanar gizo, Jinping ya ce za a karawa wasu kasashen nahiyar Afrika tsawon wa'adin biyan bashin da China ke binsu.

A cewar Jinping, kasar China a shirye take ta bawa kasashen nahiyar Afrika fifiko wajen rabon rigakafin cutar korona da zarar an kammala sarrafa shi.

A cikin jawabin da Jinping ya gabatar, ya ce kasar China ta shirya taron na hadin gwuiwa da kungiyoyin kasashen Afrika domin nuna goyon bayanta ga kasashen nahiyar Afrika a kokarin yaki da annobar korona.

Shugabannin kasashen Afrika, mambobin kungiyar gamayyar kasashen nahiyar Afrika (AU) da sauran wasu manyan masu ruwa da tsaki a sha'anin cigaban Afrika sun halarci taron.

China za ta yafewa kasashen Afrika bashi
Xi Jinping
Asali: Getty Images

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, gwamnatin kasar Amurka ta yi Alla - wadai da yawaitar kisan fararen hula a Najeriya, musamman a cikin 'yan makonnin baya bayan nan.

A cikin wani jawabi da sakataren gwamnati, Michael Pompeo, ya fitar ranar Laraba, gwamnatin kasar Amurka ta ja hankalin gwamnati a kan kisan fararen hula da 'yan bindiga da mayakan kungiyar Boko Haram ke yi a jihohin Katsina da Borno.

DUBA WANNAN: Katsina: Buhari ya aika sako ga masu zanga - zanga a kan rashin tsaro

"Mun yi Alla - wadai da wadannan kashe - kashe marasa dalili da babu wata manufa a cikinsu.

"A 'yan makonnin baya bayan nan, mayakan kungiyar ISIS a yankin Afrika ta yamma sun kai hare - hare tare da kashe fararen hula fiye da 120; da suka hada da mata da kananan yara, a jihar Borno.

"A ranar 9 ga watan Yuni, wasu 'yan bindiga sun kai hari wani kauye a Katsina tare da kashen dumbin mutane.

"Wadannan kashe - kashe sun biyo bayan harbe wani Fasto da matarsa mai juna biyu a ranar 1 ga watan Yuni da kisan wani Limami, Dagachi, da dumbin fararen hula a ranar 5 ga watan Yuni a wani rikicin kabilanci da ya barke a jihar Taraba," a cewar Pampeo.

Gwamnatin kasar Amurka ta bukaci gwamnatin Najeriya ta kara kokarinta na kare rayukan jama'a ta hanyar kawo karshen aiyukan ta'addanci tare da hukunta 'yan ta'adda.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel