Yanzu Yanzu: Buhari ya gana da wakilin Shugaban kasar China na musamman a Aso Rock

Yanzu Yanzu: Buhari ya gana da wakilin Shugaban kasar China na musamman a Aso Rock

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 5 ga watan Satumba ya yi ganawa sirri da jakada na musamman dagashugaban kasar China, Xi Jinping.

Ganawar da suka yi tare da jakadan, Mai girma Yang Jiechi, ya fara ne da misalign kare 11:30 na safe a ofishin shugaba Buhari.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruaito cewa Shugaban Najeriya da wakilin takwaransa na kasar China za su tattauna lamuran da suka shafi dangantaka tsakanin kasashen biyu.

NAN ta ruwaito cewa a yanzu haka kamfanonin kasar China na gudanar da ayyukan cigaba daban-daban na kwangila a Najeriya ciki harda zamanantar da hanyoyin tashar jiragen kasa a Najeriya da kuma sabonta da bunkasa wasu filayen jiragen sama a fadin kasar.

KU KARANTA KUMA: Dasuki ya sha kaye a kotun zaben jihar Sokoto

Har yanzu suna kan ganawar a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

A ranar Laraba, 4 ga watan Satumba ne Jiechi ya ziyarci kasar Kenya, inda ya isar da sakon Shugaban kasar na China ga Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel