Cutar Coronavirus: Ba dan Najeriya dake kasar Sin da ya kamu - Mujallar gwamnatin China

Cutar Coronavirus: Ba dan Najeriya dake kasar Sin da ya kamu - Mujallar gwamnatin China

Yayin da kasar Sin take kokarin magance cutar Coronavirus da ya addabi alummar kasar, sanarwa daga hukumar kiwon lafiyan kasar a ranar Alhamis sun tabbatar da cewa ba dan Nigeria mazaunin kasar da ya kamu da cutar.

Gwamnatin kasar Sin a mujallata kan cutar ta bayyana cewa cutar ta kama mutum 29 yan wasu kasar kuma an magance 18 daga ciki, amma ba dan Nigeria a ciki.

Mujallar ta bayyan cewa “29 yan wasu kasa dake kasar Sin sun kamu da cutar. An magance 18 an sallame su daga asibiti, 2 sun mutu sannan 9 suna karkashin kulawa.”

Lokacin da annobar cutar ta shigo kasar Sin, yan wasu kasashe da yawa hadi da Nigeria sun roki gwamnatin su data fitar dasu daga kasar.

Amma gwamnatin Nigeria tayi kunnan shegu da maganarsu tace bata ga dalilin yin haka ba.

Cutar Coronavirus: Ba dan Najeriya dake kasar Sin da ya kamu - Mujallar gwamnatin China
Cutar Coronavirus: Ba dan Najeriya dake kasar Sin da ya kamu - Mujallar gwamnatin China
Asali: UGC

KU KARANTA Gwamnatin tarayya zata gina masana’anta a kowacce mazaba a Najeriya - Minista

A bangare guda, Gwamnatin tarayya tayi alkawarin baiwa duk wani masanin kimiyan Najeriyan da ya samo maganin rigakafin cutar Coronavirus kyautan kudi Milyan N36m.

Ministan Kimiya da fasaha, Ogbonnaya Onu, ya yi wannan alkawari ne a Abuja ranar Alhamis a taron walima da aka shiryawa daya daga cikin manyan diraktocin ma’aikatar, Injiniya A Oyefeso, wanda yayi ritaya.

Onu ya ce akwai bukatar Najeriya ta yi nazarin wuri gabanin sauran kasashen duniya wajen kare kanta da cutar.

Ya ce gwamnatin za ta bada gudunmuwar kudi ga masana kimiyan Najeriya wajen samar da magani ga wasu cututtuka da suka addabi kasar.

Yace “ Muna alkawari ga kowani masanin kimiyya a Najeriya da zai iya samar da rigakafin Coronavirus kudi N36m.“

“Muna da magunan gargajiya da dama a kasar nan, da yiwuwan maganin cutar na gonakinmu.“

“Muna kalubalantar masana kimiyanmu su samo maganin cutar kuma lallai kasar zata karrama su.“

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel