Sabon Rikici a Najeriya Yayin da Kungiyar Likitocin Najeriya Suka Ayyana Fara Zanga-Zanga

Sabon Rikici a Najeriya Yayin da Kungiyar Likitocin Najeriya Suka Ayyana Fara Zanga-Zanga

  • Kungiyar likitoci a Najeriya ta ce za ta gudanar da kazamar zanga-zanga nan ba da jimawa ba a kasar
  • Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskatar matsalar tattalin arziki da talauci a Najeriya
  • Yanzu haka, ba a kammala da ASUU da sauran malaman jami'a ba, ga batun likitoci na ci gaba da kamari

FCT, Abuja - Kungiyar Likitoci ta Najeriya (NARD) ta ayyana yin zanga-zanga a duk fadin kasar a kowace rana tare da mamaye cibiyoyin kiwon lafiya na tarayya.

A wata sanarwar da ta fitar a ranar Asabar, kungiyar da a halin yanzu take yajin aiki a fadin kasar ta ce za a fara zanga-zangar ne a ranar Laraba 9 ga watan Agusta da karfe 10:00 na safe.

Sanarwar ta fito ne bayan taron majalisar zartarwa ta kasa na kungiyar a ranar Asabar, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ba Kanwar Lasa: Kididdigar Karfi, Iko da Makamai Tsakanin Sojin Najeriya da Na Nijar

Likitocin Najeriya za su yi zanga-zanga
Zanga-zanga za ta barke tsakanin likitocin Najeriya | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Yadda za a yi zanga-zangar

Hakazalika, sanarwar fara zanga-zangar an tura ta ne ga Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban kungiyar, Dr Orji, Emeka Innocent, da Sakatare Janar, Dr Chikezie, Kelechi ne suka sanya hannu kan sanarwar.

NARD ta ce matakin zanga-zangar ya zama dole don neman a biya musu bukatunsu wanda ma’aikatar ilimi ta tauye, TheCable ta ruwaito.

Lokaci ya yi da ya kamata a gyara, inji NARD

Ta kuma bayyana cewa, lokaci ya yi da ya kamata ta nuna wa duniya abin da yake faruwa da kuma irin rashawar da ake aikatawa da ma'aikatar lafiya ta Najeriya.

Najeriya dai na yawan samun matsala da ma'aikata, kasancewar yadda ake samun karancin albashi da jin dadin ma'aikatan gwamnati.

Har yanzu ba a kammala biyan bukatun malaman jami'a ba a kasar na, lamarin da ke kara daukar hankali.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Atiku Abubakar Ya Sa Labule da Wasu Gwamnoni 7 a Abuja, Sahihan Bayanai Sun Fito

Yadda batun yajin aiki ya taso

A wani labarin, a ranar Laraba, kungiyar NARD ta likitoci su ka tsawaita wa’adin da su ka ba gwamnatin tarayya domin a biya masu bukatu ko su yi yajin-aiki.

Premium Times ta ce likitocin kasar sun kara makonni biyu kamar yadda su ka sanar a karshen taron majalisar koli ta NEC da aka yi ta yanar gizo.

Jawabin bayan taron da aka fitar ya nuna an zargi gwamnatin tarayya da kin cika alkawuran da ta dauka bayan zaman 19 ga watan Mayu da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.