Bazoum: Hambararren Shugban Nijar Ya Roki Amurka da Wasu Kasashe Su Kai Masa Ɗauki

Bazoum: Hambararren Shugban Nijar Ya Roki Amurka da Wasu Kasashe Su Kai Masa Ɗauki

  • Muhammed Bazoum, shugaban Nijar da sojoji suka kifar ya aike da sako ga Amurka da sauran ƙasashen duniya
  • Hambararren shugaban kasar, a wani gajeren sako, ya ce yana fargabar ƙasarsa ka iya faɗawa sharrin Rasha
  • Bazoum ya yi gargaɗin cewa sakamakon da zai biyo baya ba zai yi kyau ba ga Nijar da sauran ƙasashen Afirka matuƙar sojoji suka yi nasara a Nijar

Shugaba Muhammed Bazoum, wanda sojoji suka kifar da gwamnatinsa a Nijar, ya yi kira ga ƙasar Amurka da sauran al'ummar duniya su kawo wa Nijar ɗauki.

Bazoum, wanda har yanzu yake tsare a hannun sojojin da suka masa juyin mulki, ya buƙaci kasashen duniya su dawo da mulkin demokuraɗiyya a Jamhuriyar Nijar.

Shugaban Jamhuriyar Nijar da aike da saƙo ga Amurka.
Bazoum: Hambararren Shugban Nijar Ya Roki Amurka da Wasu Kasase Su Kai Masa Ɗauki Hoto: ECOWAS
Asali: Twitter

A rahoton BBC, shugaban Nijar wanda ya rasa kujerarsa makon da ya gabata, ya ce yana rubuta wannan sakon ne a matsayin wanda ke tsare.

Kara karanta wannan

Jerin Matakai 7 Masu Tsauri da Shugaba Tinubu da ECOWAS Ke Shirin Ɗauka Kan Jamhuriyar Nijar

Ina tsoron Nijar ta faɗa karkashin ikon Rasha - Bazoum

Shugaban ya kuma yi gargadin cewa yankin na iya fadawa karkashin ikon Rasha ta hanyar kungiyar Wagner, wadda tuni ta fara aiki a kasashen da ke makwabtaka da Nijar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ana fama da tashe-tashen hankula a kasar da ke yammacin Afirka tun bayan hambarar da gwamnatin Bazoum da sojoji suka yi.

Shugaban gwamnatin soji a Nijar ya sanar da cewa sun janye jakadun ƙasar na ƙasashen Najeriya, Amurka, Faransa da Togo. Ya ƙara da cewa sun kore su daga aiki.

Wannan na zuwa ne a lokacin da aka rahoto jakadan Nijar a ƙasar Amurka, Kiari Liman-Tinguiri na cewa ya kamata sojojin da suka yi juyin mulki su sun cewa haƙarsu ba zata cimma ruwa ba.

Jamhuriyar Nijar tana da makamashin Uranium mai ɗumbin yawa kuma makamashin yana da muhimmanci a ƙarfin nukiliya, Aljazeera ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sheikh Rijiyar Lemu Ya Aike da Saƙo Mai Muhimmanci Ga Shugaba Tinubu Kan Tura Sojoji Jamhuriyar Nijar

A wani rubutun da ya yi a shafin jarida, hambararren shugaban ƙasar ya yi gargaɗin cewa idan masu juyin mulkin suka yi nasara, sakamakon da zai biyo baya ba zai yi kyau ba.

Jerin Matakai 7 Masu Tsauri da Shugaba Tinubu da ECOWAS Ke Shirin Ɗauka Kan Jamhuriyar Nijar

A wani rahoton kuma A yunkurin dawo da zaman lafiya da mulkin demokuraɗiyya, ECOWAS ta kira taro kuma ta cimma matsayar ɗaukar matakai 7.

Matakan na kunshe ne a cikin wata wasika da shugaba Tinubu ya aika majalisar dattawa ranar Juma’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262