Juyin Mulki: Jerin Matakai 7 da ECOWAS Karkashin Tinubu Ke Shirin Dauka Kan Nijar
Juyin mulkin da aka yi kwanan nan a jamhuriyar Nijar, wanda ake ganin koma baya ne ga demokuraɗiyya ya fusata ƙungiyar raya ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS).
Channels tv ta tattaro cewa karkashin jagorancin shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ƙungiyar ECOWAS ta amince da ɗaukar tsauraran matakai guda 7 kan jamhuriyar Nijar.
A taron ta na baya-bayan nan, ECOWAS ta aminta da ɗaukar matakan a yunkurin dawo da mulkin Demokaraɗiyya a Nijar, ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar.
Matakan da aka ayyana, tun daga na diflomasiyya har zuwa yiwuwar sanya takunkumi, sun nuna yadda kungiyar ECOWAS ke kokarin kare mutuncin dimokradiyya a yankin.
A wannan shafin mun haɗa muku matakai bakwai da ECOWAS ta yanke shawarar ɗauka a wani yunƙuri na kawar da wannan juyin mulki da sojoji suka yi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Matakan na kunshe ne a cikin wata wasika da shugaba Tinubu ya aika majalisar dattawa ranar Juma’a, inda ya sanar da majalisar shawarar da kungiyar ECOWAS ta yanke kan halin da ake ciki a Jamhuriyar Nijar.
A cewar Tinubu, ECOWAS karkashin jagorancinsa ta yi Allah wadai da juyin mulkin gaba daya tare da kudurtan neman dawo da gwamnatin da aka zaba ta hanyar dimokradiyya.
Jerin matakai 7 da ECOWAS ta yanke shawarar ɗauka
Rahoton Daily Trust ya ce a yunkurin dawo da zaman lafiya da mulkin demokuraɗiyya, ECOWAS ta kira taro kuma ta cimma matsaya kamar haka:
1. Kulle dukkan wasu iyakoki da ƙasar Nijar tare da dawo da ayyukan motsa jikin sojoji a bakin iyakokin.
2. Katse wutar lantarƙin da ake kai wa jamhuriyar Nijar.
3. Tattara tallafin kasashen duniya domin tabbatar da an aiwatar da shawarwarin da ECOWAS ta yanke a zamanta.
4. Hana dukkan jiragen sama shiga ko fitowa daga jamhuriyar Nijar.
5. Dakatar da kayan abincin da ke hanyar zuwa Nijar musamman daga jihar Legas da bakin teku.
6. Wayar da kan ‘yan Najeriya su san muhimmancin wadannan matakai musamman ta kafafen sada zumunta.
7. Ɗaukar matakin soji kan masu jurin mulkin idan sun yi taurin kai.
Sanatocin Arewa Ba Su Yarda Tinubu Ya Shiga Yaki da Kasar Nijar ba
A wani rahoton kuma Sanatocin da su ka fito daga jihohin Arewacin Najeriya, ba su gamsu da maganar daukar makami a kan sojojin Jamhuriyyar Nijar ba.
Wakilan jihohin Arewa a majalisar dattawa, sun fadawa Mai girma shugaban Najeriya cewa ya sake nazari kan maganar shiga Nijar da yaki.
Asali: Legit.ng